TARIHIN UNGUWAR DARMA KATSINA.
- Katsina City News
- 12 Dec, 2024
- 159
Darma tana daya daga cikin Unguwannin dake haben birnin Katsina. Tsohuwar Unguwace wadda ta kafu tun lokacin Sarakunan Habe, lokacin da ake gina Ganuwar Katsina wajen shekarar (1452-1475). A dai dai wannan lokacinne Kasar Katsina ta rinka karbar Baki Yan Kasuwa da masu sana'oi. Wannan daliin ya sanadiyyar kafuwar Unguwar Darma. Darma tana daya daga cikin Unguwannin da masu sanaar Darma suka kafa a wancan Lokacin, daga sanaar Darmanne ma aka samu sunan Unguwar Darma.
Amma daga baya sai bakin Yan Kasuwa da Malamai suka rika Zama Unguwar har takai sun mamaye masu sanaar kirar. Daga cikin Malaman da suka zauna a Darma akwai wani Shahararren Malami da ake Kira Malam Muhammadu Bakogayi, Wanda yawo Kaura daga Kogo ta Kasar Faskari zuwa birnin Katsina, a lokacin Mulkin Dallazawa. Daga cikin Yayan wannan Malami akwai Malam Salihu Gatarin Baki, Wanda ya shahara kwarai akan harkar Malanta a zamanin Sarkin Katsina Muhammadu Dikko (1906-1944). Daga cikin jikokin Salihu Gatarin Baki akwai Professor Mannir Mamman Darma, da Abba Abu Rafin Dadi ta wajen Mahaifiyar shi, da sauransu.
Daga cikin mutanen da suka yo Kaura daga Kogo zuwa Darma ta Katsina akwai wata Attajiri Kuma babbar Yar Kasuwa, wadda ake Kira da Madiga Indo. Madiga Indo ta shahara wajen kasuwancin ta acikin Karni na sha Tara ( K19). Madiga Indo ta kafa wata babbar Turaka ta bayi a Rimin Sambani, cikin Darma. Rimin Sambani wani Shahararren Rimi ne da akayi a Darma. Wurin Mahada ce ta Fatake da Yan Kasuwa iri- iri da suka fito daga Kasashe daban daban. Madiga Indo ta kasance tana cinikin Bayi daga Katsina zuwa manyan kasuwanni irin su Zurmi da sauransu. Ance ta zauna Katsina daga shekarar 1870-1906. A cikin shekarar 1906 ne ta tashi daga Katsina ta koma Lokoja, daliin tube Sarki Abubakar da Turawan Mulkin Mallaka sukayi cikin shekarar 1905.
Baya ga Madiga Indo anyi Kuma wata babbar Yar Kasuwa a Darma din Mai suna Hajiya Baika. An haifi Hajiya Baika acikin shekarar 1889. Baika Matar wani babban Dan Kasuwa ne Mai suna Abba Saude. Abba Saude dane ga wani babban Attajiri Kuma Dan Kasuwa a Gonja, Mai suna Alhaji Muhammadu. Abba Saude Yana fatauchin kaya daga Katsina zuwa Gonja, Kuma idan zai tafi tare da Matar shi Baika yake tafiya.Ta hakane Baika ta koyi Kasuwanci ta hanun mijinta, ta rinka tafiya da kaya kamar Daddawa, da sauran kayan Miya daga Katsina zuwa Gonja, idan Kuma zata dawo Katsina sai ta sawo irin kayayyakinsu ta sayar a Katsina. Da hakane Baika har takai tafi mijinta Abba Saude karfi wajen Kasuwa. Tarihi ya nuna Hajiya Baika itace Attajjra ta biyu data fara sayen Mota a Katsina, bayan Abu Kyahi na Kofar sauri ya saya. Wasu daga cikin Yayan Baika sun hada da Alhaji Salisu Madugu Darma, Raben Baika, Alhaji Iron Baba, Dahiru Saude da sauransu. Wasu daga cikin Jikokin Baika sun hada da Ali Madugu, Usman Madugu, Lawal Audu, Engineer Muttaka Rabe Darma da sauransu.
Akwai kuma Gidan Baraya Titimi a Darma, Wanda shima asalin shi Mutumin Kogo ne ta Kasar Faskari. Ance Sarkin Katsina Muhammadu Dikko (1906-1944) ya nadashi Sarautar Barayan Katsina.
Alh. Musa Gambo Kofar Soro.