Gwamnatin Tarayya Ta Fitar Da Jerin Sunayen Masu Neman Aikin Hukumar Kashe Gobara
- Katsina City News
- 08 Dec, 2024
- 140
Gwamnatin Tarayya ta fitar da jerin sunayen wadanda suka yi nasara a daukar ma’aikata na Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya (FFS).
A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Asabar, Sakatare na Hukumar Kula da Tsaro, Gyaran Hali, Kashe Gobara, da Shige da Fice, Ja’afaru Ahmed, ya ce masu nema za su iya duba jerin sunayen a shafin yanar gizon hukumar.
“Masu neman aikin da suka cika takardun daukar ma’aikata na Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya yanzu suna iya ziyartar shafin yanar gizon hukumar a www.cdcfib.career daga ranar Litinin, 9 ga Disamba, 2024, don tantance matsayinsu da kuma duba takarda gayyatarsu,” in ji sanarwar.
“Masu neman aikin za su sanya riga da wando fari sannan su kawo takardunsu na asali da kwafi. Dole ne kuma su tabbatar da sun halarci wurin a ranar da aka ayyana a cikin takardar gayyatarsu.”
“Hukumar Kula da Tsaro, Gyaran Hali, Kashe Gobara, da Shige da Fice tana sanar da masu neman aikin a Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya (FFS) su ziyaci shafin yanar gizon hukumar a www.cdcfib.career daga ranar Litinin, 9 ga Disamba, 2024, don tabbatar da samun nasarar su a matakin karshe na tantancewa." Inji sanarwar