Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Kungiyar Citizens Participation Against Corruption Ta Gabatar Da Ƙasida
- Katsina City News
- 06 Dec, 2024
- 225
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Comrade Bishir Dauda Sabuwar Unguwa Katsina
A cikin wani muhimmin taro da aka gudanar a NUJ Secretariat ranar juma'a 6 ga watan Disamba, Comrade Bishir Dauda Sabuwar Unguwa, shugaba a kungiyar "Citizens Participation Against Corruption Initiative", ya gabatar da wani rahoto mai zurfi kan yaki da cin hanci a jihar Katsina daga shekarar 2023 zuwa 2024. Wannan rahoto ya mayar da hankali kan matakan da aka dauka, tasirin su, da kuma shawarwarin da za su taimaka wajen cimma nasarori masu dorewa.
A jawabinsa, Kwmarat Bishir ya jinjina wa Gwamna Dikko Umar Radda, wanda aka rantsar a matsayin gwamna na huɗu na dimokuradiyya a jihar Katsina ranar 29 ga Mayu, 2023. Ya bayyana cewa, tun daga lokacin, gwamnan ya mayar da hankali wajen magance matsalolin jihar, ciki har da inganta ilimi, kiwon lafiya, tsaro, da rage talauci. Sai dai, ya jaddada cewa babu wata nasara da za ta tabbata matukar ba a yaki yi cin hanci da rashawa ba.
Malam Bishir ya kuma yi tsokaci kan kalubalen yaki da cin hanci, yana mai cewa, yaki da wannan muguwar dabi’a ya zama wajibi ba kawai ga gwamnati ba, har ma ga daukacin al’umma.
A cewar Malam Bishir, cin hanci ya zarce abin da aka saba danganta da karɓar rashawa kawai. Ya kawo misali da kalaman marigayi Farfesa Femi Odekunle, wanda ya bayyana cin hanci a matsayin duk wani aiki da ke ba wani riba ta haram, amma ya cutar da moriyar jama’a gaba ɗaya.
Rahoton ya bayyana wasu daga cikin matakan da gwamnatin jihar Katsina karkashin Gwamna Radda ta ɗauka wajen yakar cin hanci, ciki har da:
Samar da Asusun Gwamnati (TSA): Wannan tsari ya rage asarar kudade tare da kara inganta kudaden shiga, Kafa Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaki da Cin Hanci, Hukumar ta samu goyon baya daga gwamnati, kuma tana da kyakkyawan fata wajen kawar da cin hanci a jihar, Shiga Yarjejeniyar Gwamnati (OGP), Wannan tsari ya kara jan hankalin jama’a wajen shiga ayyukan gwamnati da samar da gaskiya, Digitization na Karɓar Haraji, Wannan mataki ya rage satar kudaden gwamnati tare da habaka kudaden shiga na cikin gida, da Ƙarfafa Ayyukan Zakka da Wakafi, Wannan tsarin yana rage rashin daidaito a cikin al’umma. Ya bayyana.
Rahoton ya jaddada cewa matakan yaki da cin hanci a Katsina sun fara samun nasarori, musamman wajen kawar da asarar kudade da kara inganta ayyukan gwamnati. Sai dai, wasu matsaloli sun kasance, ciki har da rashin isasshen kudade ga hukumomin da ke yaki da cin hanci da kuma karancin horarwa ga ma’aikata.
Kwamarat Bishir ya bada shawarwari da zasu inganta gudanarwa cewa; A kafa kwamiti na OGP tare da tsara tsare-tsaren aiki, A fara wallafa sakamakon zaman majalisar zartarwa a jaridu, A gudanar da taron sauraron ra’ayoyin jama’a a duk kananan hukumomi 34, A ci gaba da bai wa ma’aikatan gwamnati nagari lada don karfafa musu gwiwa.
Malam Bishir ya yi kira ga iyaye, malamai, da shugabannin addini da su taimaka wajen tarbiyyar yara da koyar da su muhimmancin gaskiya da rikon amana. Ya kuma bukaci gwamnati da ta zage damtse wajen amfani da fasahar zamani don kawar da cin hanci.
Daga karshe, ya jaddada cewa yakar cin hanci ba na gwamnati kawai ba ne, ya zama wajibi ga kowa da kowa. "Idan har za mu hada kai, za mu iya ganin Katsina ta zama abar alfahari," in ji Malam Bishir.