Zaman Lafiya Da Cigaban Yankin Arewa Ne Burin Mu --Inji Shugaban kungiyar Rebuild Arewa Initiative Balarabe Rufai
- Katsina City News
- 06 Dec, 2024
- 193
Kungiyar sake gina Arewacin Najeriya,mai suna Rebuild Arewa Initiative for Development,ta bakin shugabanta, Balarabe Rufa'i ta ce assasa zaman lafiya,hadin kai da ci gaba Arewa yasa suka kafa Kungiyarsu.
Ya ce sun zo Jihar Katsina ne, saboda muhimmancinnta ."Babu wata gwagwarmaya da mutum zai yi da sunan Arewa ba tare da ya ziyarci jihar Katsina ba. Saboda jiha ce dake da masu ilimi da kusoshin gwamnati."
Kungiyar ta bayyana hakan ne a lokacin wata ziyarar bangirma da shugabannin kungiyar suka kai ma mai martaba sarkin Katsina, Alhaji Dokta Abdulmumini Kabir Usman, yau a fadarsa.
A nashi jawabin mai martaba sarki ya sanya ma kungiyar albarka, sannan ya Kara da cewa Arewa na bukatar kungiyoyi irin wannan, domin ceto yankin daga matsaloli,musamman matsalar tsaro. Wannan ziyarar na ji dadin ta kwarai Kuma za mui aiki da ku.
Hakazalika mai martaba Sarki ya bukaci kungiyar ta bashi mutane biyu domin kafa kwamitin da zai yi fafutikar dawo da martabar yankin Arewacin Najeriya.
A karshe Sarkin ya nuna goyon bayansa ga kungiyar tare da yi masu fatan alkairi sannan yayi adduar da samun nasara ga kungiyar kan ayyukan da ta a gaba.