BAUTAR TAMBARI

top-news

Idan aka ce bauta, ana nufin irin hidimar da ake yi masa bayan an gama haɗashi.

Cikin abubuwan da ake yi masa akwai,
 : Zumuwa Farar saƙa
 : Man shanu
 : Kayan yaji irin su cita, karamfani da dai sauransu.

Yanda ake yi za'a dake/niƙa sai a haɗe su tare da zumar da manshanun, sai a zuba masa ta wata yar ƙofa kaɗan.

Idan aka kwarara masa ta wannan ƙofa sai a kwantar da shi a kifa shi domin fatar ta tsotsa.

Bayan nan sai a hura wuta a kanga Tambarin ya sha wutar Saboda fatar ta sake ya yi laushi.

 *MAKAƊIN TAMBARI*

Makaɗi shine abinda ake amfani da shi wajen Buga Tambari da shi, a can da wancan zamanin da jijiyar Raƙumi ake amfani da ita sai a ɗunke da fatar sa, amma yanzu ana amfani da Dorina sai a yanyankata.

 *RABE RABEN KIDAN TAMBARI YA KASU KASHI BIYU 2*

1.Akwai wanda ake cewa, Talinjin Talinjin.
   Ma'ana ana cewa ( Agaishe ka Sarki )

Amma shi irin wannan kiɗan an ce har yanzu irin shi ne masarautar Sarkin Gobir na Tsibiri Madawa dake ƙasar Niger suke yi komi da komi, shima har yanzu ba'a hakaito asalin shi ba.

2. Kwatakwal, shinkuma Ɗan Zariya ne, wannan kiɗan asalin shi daga masarautar Zazzau ya ke.

Ma'ana ana cewa,

Gyara garin ka sarki Gyara garin ka.
Baƙon Dole sarki Baƙon Dole.
Kafi Talauci sarki Kafi Talauci.

Wannan shine ma'anar.