NAWOJ Katsina Ta Taya Sabon Shugaban NUJ Murnar Zaben Sa
- Katsina City News
- 29 Nov, 2024
- 128
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, (Katsina Times)
Kungiyar Mata 'Yan Jarida ta Najeriya (NAWOJ), reshen jihar Katsina, ta taya Alhassan Yahya Abdullahi murnar lashe zaben sa a matsayin sabon shugaban Kungiyar 'Yan Jarida ta Najeriya (NUJ).
A cikin wata sanarwa da ta fitar yau, Shugabar NAWOJ Katsina, Hannatu Mohammed, ta bayyana farin ciki da alfahari da wannan gagarumin nasara da Alhassan Yahya Abdullahi ya samu. Ta yaba da sadaukarwar sa ga aikin jarida da jajircewar sa wajen kare hakkoki da jin dadin 'yan jarida a fadin kasa.
"Muna matukar farin cikin ganin Alhassan Yahya Abdullahi ya zama sabon shugaban NUJ," in ji Hannatu Mohammed. "Jagorancinsa da hangen nesansa tabbas za su kawo sauyi mai kyau da ci gaba a fannin aikin jarida. Muna fatan yin aiki tare da shi domin kare hakkin 'yan jarida, musamman mata, a wannan masana'anta."
NAWOJ Katsina ta nuna kwarin gwiwa cewa, karkashin jagorancin sabon shugaban, kungiyar za ta samu karin ci gaba da bunkasa harkokin jarida a Najeriya.