TATSUNIYA: Ga Ta Nan, Ga Ta Nanku, Dan Agwai Da Kura
- Katsina City News
- 24 Nov, 2024
- 160
Zaharaddeen Ishaq Abubakar (Katsina Times)
Akwai wani dan Agwai yana kiwon dan akuyarsa, har ya girma sosai. Sai wata rana, ya ɗauki dan akuyarsa, ya kai shi kasuwa. Namun daji da yawa sun shiga wajen saye, amma da zarar sun ji labarin dan akuyar, sai su wuce, su ki saye.
Ana nan ana nan, har labari ya kai ga kunnuwan Kura, wadda ke cikin rashin hankali. Sai ta shirya, ta tafi kasuwa don cinikin dan akuyar. Kura ta ga dan akuyar yana da kiba, kuma tana so ta siya.
Sai ta tambayi dan Agwai: "Nawa kudin dan akuyan nan?"
Dan Agwai ya amsa da cewa: "Ni fa kokawa za ki yi da ni na kwana bakwai a jere. Idan kullum kina kawar da ni har kwana bakwai, to dan akuyar zai zama naki. Idan kuma kin kasa, to sai mun ci gaba da kokawa har sai ranar da kika sami nasara."
Kura ta ce: "To na yarda." Aka tara 'yan kallo, aka bayyana cewa Kura za ta sayi dan akuyar Dan Agwai. Kowa ya share wuri, aka zauna don kallon cinikin.
Can sai Kura ta shirya, ta fito fage suka kama kokawa da Dan Agwai. Kura ta doke Dan Agwai, ta ci nasara har kwana shida. A rana ta bakwai, sai Dan Agwai ya doke Kura, ya yi mata duka har ta kasa tashi. Da ta murmure, da kyar ta tafi gida. Sai ta ce: "Yau ban samu nasara ba."
Washegari ta tafi, Dan Agwai ya sake doke ta da kasa har ta suma. An kai ta gida, da safen gobe sai ta ce da 'ya'yanta su boye ta a cikin rumbu, kuma idan an zo neman ta, su ce ta tafi.
Dan Agwai ya je gidan, ya yi sallama, amma sai 'ya'yanta suka ce mahaifiyarsu ta tafi. Sai Dan Agwai ya ce: "To, bari in bude rumbun, in ga hatsin da ke ciki."
Kafin yaran su hana, Dan Agwai ya bude rumbun, ya leka, sai ga Kura a ciki. Ya ciro ta, ya kai ta fagen kokawa. Suka fafata, ya dauke ta sama, ya dankare ta da kasa. Daga karshe, Kura ta koma gida da rarrafe.
Da 'ya'yanta suka ga haka, sai suka ce: "Baba, wannan Dan Agwai zai kashe ki, sai mun nemi asirin da zai sa ki samu nasara."
Washegari, suka tafi gidan boka, suna neman asiri. Boka ya ce: "Babu magani, amma akwai wata dabara. Akwai wani mutum mai suna Mai-barci-bana-ya-tashi-badi, yana can a dakinsa yana barci. Za ku samu garwashin wuta, ku tafi ku ce wa Dan Agwai: 'Ga wani zai yi cinikin dan akuyarka da kokawa.' Idan kun isa dakin Mai-barci-bana, sai ku zuba barkono a wuta, ku fita."
Da suka tafi, suka bi umarnin boka. Suka kawo Dan Agwai dakin Mai-barci-bana, suka kulle su. Sai hayakin barkono ya tashi. Mai-barci-bana ya tashi, ya ji zafin hayakin, sai ya kashe Dan Agwai. Ya fita daga dakin, ya ga Kura tana jiran shi. Ya ce mata ta raka shi farauta, yana jin yunwa. Kura ta yarda.
Suka tafi cikin daji, suka tarar da mutane masu noma a gonar Sarki. Mai-barci-bana ya ce: "Ga nama, amma ba zai ishe ni ba." Ya kama mutanen ya murde wuyan kowanne, ya tara tace zai gasa, amma babu wuta. Daga nan, ya hura bakinsa, wuta ta fito, ya gasa mutanen. Kura ta ce: "Tun da shi ne babba, ya fi ci." Yana cin naman mutanen har ya kare, Kura ba ta ci ba. Bayan ya gama, sai ya sa Kura ta samo masa tsinken sakatar hakora. Ta samo, ta ba shi.
Daga nan, Mai-barci-bana ya ce: "Mu tafi rafi mu sha ruwa." Kura ta ki, sai ya fara sha. Da ya sha, sai ya shanye duk ruwan rafi.
Abubuwan da Labarin Yake Koyarwa:
- Kwadayi yana kawo wahala.
- Wani lokaci, dabara ta fi karfi.
- Duk inda aka samu zalunci, za a samu wanda zai fi zalunci.
- Kaddara tana fi fata.
Daga Littafin Taskar Tatsuniyoyi Na Dakta Bukar Usman