Kungiyar Dattawan Arewa ta yi watsi da kudurin dokar sake fasalin haraji na Tinubu
- Katsina City News
- 24 Nov, 2024
- 150
Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta yi watsi da kudurin dokar sake fasalin haraji, tare da gargadin cewa yana barazana ga hadin kan kasa. Kungiyar ta soki yadda aka aiwatar da ita, inda ta yi zargin cewa an mayar da masu ruwa da tsaki ciki har da mambobin majalisar tattalin arzikin kasa a gefe yayin gudanar da aikin.
Shugaban kungiyar Dattawan Arewa, Farfesa Ango Abdullahi, bayan taron kwamitin amintattu na karo na biyu na shekara-shekara, a Abuja ya bayyana haka.
Kungiyar ta yabawa kungiyar gwamnonin jihohin Arewa da kuma majalisar sarakunan arewacin Najeriya da suka nuna adawa da kudurin, inda suka bayyana matsayarsu a matsayin ‘yan kishin kasa, tare da yin kira ga ‘yan siyasar Arewa a majalisar dokokin kasar da su tofa albarkacin bakinsu.
Taron ya yi nuni da cewa, a halin da ake ciki yanzu, dokar sake fasalin haraji an yi shi ne da nufin tursasawa yan kasar, kuma hakan barazana ce ga hadin kanmu da hadin kan kasa.
"Taron ya ci gaba da jawo hankulan mutane kan hanyar da ba ta dace ba da kuma yadda aka sanya dokar sake fasalin haraji a kan al’umma, ba tare da ba da damar shigar da masu ruwa da tsaki ba, kamar yadda ya sanya mambobin majalisar tattalin arzikin kasa cikin duhu.
“Majalisar, ta yi Allah-wadai da kakkausar murya, da irin hasarar murya da aka yi a kan wannan batu na yawan zababbun ’yan siyasa da suka fito daga yankin, tare da yi musu gargadi da kakkausar murya.
Kungiyar ta NEF ta bukaci ‘yan Arewa da su kara taka tsan-tsan wajen kare hakkinsu, musamman a lokacin zabe, ta kuma yi gargadin cewa kada su fada cikin magudin shugabanni marasa kishin kasa.