Kwamitin Tattalin Arziki ta Kasa (NEC) Ya Dauki Matakan Magance Kalubalen Da Ake Fuskanta a Fannin Samar da Wutar Lantarki a Najeriya.
- Katsina City News
- 22 Nov, 2024
- 32
A taronta karo na 146, Majalisar ta NEC ta kuduri aniyar haɓaka sabbin dabarun hana faduwar turakun wutar lantarki da ake fuskanta a Najeriya.
Majalisar wadda ke karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ta fitar da jadawalin shawarwarin da suka hada da Kafa wani kwamiti bibiyar gyaran wutar na ƙasa, karkashin jagorancin gwamnan jihar Cross River, Bassey Otu.
Sabon kwamitin zai mai da hankali wajen tuntubar jihohi da sanya ido kan ganin an aiwatar da dokar sake fasalin wutar lantarki ta 2023 wadda gwamnati ta amince da ita.
Hukumar ta kuma jaddada bukatar yin garambawul ga tsarin rarraba wutar lantarki, ta yadda za a bai wa jihohi damar samar da wutar lantarki mai sauki ga yankunansu.
Mataimakin shugaban kasar, Kashim Shettima ya jaddada cewa samar da waddataccen makamashi hakki ne da ya rataya a wuyan gwamnati ta samar duba da kasancewarsa kahon zuciyar tattalin arziki.
Majalisar ta kuma bukaci jihohi da su sanya hannu a cikin shirin samar da shiyoyin ma'aikatun sarrafa kayan noma na Agro-Industrial Processing Zones (SAPZ), wanda ke da nufin bunkasa noma da masana'antu, kazalika hukumar ta amince da nadin mutanen da za su yi aiki a majalisar gudanarwa ta hukumar saka hannun jari ta kasa wato (NSIA)
Majalisar ta rufe zamanta da bayar da umarni ga hukumar kula da kayayyakin more rayuwa ta kimiyya da fasaha ta kasa, wato (NASENI) da ta gyara taraktoci da sauran injinan noma tare da habaka kafa masana'antar batirin lithium
Rahma Abdulmajid
Mai taimaka wa Shugaban Kasa kan harkar Radio da yada labarai, Ofishin Mataimakin shugaban kasa