Yau Kwanakinta 4 A Hannun Masu Garkuwa Da Mutane.

top-news

Yanda Masu Garkuwa Da Mutane Suka Saci Yarinya Mai- Shekaru 3 Da Haihuwa Awata Unguwar Garin

Awata zantawa da mukayi da mahaifin yarinyar da masu garkuwa da bil'adam suka sace Malam Yusuf ya bayyana mana da kimanin karfe 3:00 daren Laraba washe garin Alhamis daya gabata, Yana cikin barci yaji motsi akan katangar gidan shi,bayan farkawarshi ne ya leko domin ganin meke motsi, sai yaga Mutum ya hauro saman katangar gidanshi.

Mahaifin yarinyar ya ce ganin haka yafara neman taimako ga Allah ta hanyar yin Sallallami Waɗanda addinin Musulunci ya tanadar da kuma Ardu'o'i.

Malam Yusuf ya cigaba da cewa bayan dirowar shi ne sai mutum na biyu shima ya samu damar shiga gidan, ayayin dayaga hakane fa yafara kira Yan uwa dasu kawo mashi dauki, duk da cewa gidan shi bashida nisa da ofishin yan Sandan garin na Kankara, Amma wanda hakan baisamu ba, Koda na mutanen Unguwa.

Cikin firgita yasamu wata kafar fita tareda matarshi inda ita kuma yarinyar da ake garkuwa da ita tana ta barci abinta kuma yace basuyi tunanin zasu kula taba, duba karantar ta ashekaru.

Masu garkuwa da mutanen sunyi Amfani da makami wajen sare makaran tagar dakin da yarinyar take kwance kafin su shiga ciki.

Malam Yusuf ya tabbatar da yayi kokarin sanar da Jami'an tsaron yan Sanda bayan ta fita alokacin ta hanyar zuwa ofishin su amma kafin zuwan Jami'an tsaron harsun gama sun tafi jeje.

Awani bangaren kuma masu garkuwa da bil'adaman sun sace matan wani makwabcin wannan Bawan Allah aduk acikin wannan daren guda biyu tareda goyon Yaro daya.

Wani mazaunin wannan unguwa Mai suna Hon. Umar Nagurbi yakoka akan rashin isasshen tsaro da Unguwar bata samu, duba da yadda take abakin daji.

Wannan yasa yayi kira ga masu ruwa da tsaki na Karamar hukumar ta Kankara dasu cigaba ta biyawa Jami'an tsaron bukatun su afannin abubuwan kayan aiki don tabbatar da tsarone.

Daga Karshe muna Addu'a Allah ubangiji ya ceto mana dukkanin ysn uwanmu dake hunnun Waɗannan Mutane.

Sukuma Idan masu shiryuwane Allah yashirya su idan kuma bamasu shiryuwane ba Allah kasan yadda zakayi dasu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *