NNPC Ta Kaddamar da Sabon Man Fetur Mai Suna Utapate a Kasuwar Duniya
- Katsina City News
- 20 Nov, 2024
- 63
OML 13 Na Shirin Samar da Ganga 80,000 a Rana Zuwa Karshen 2025
Katsina Times
A wani muhimmin mataki da zai kara bunkasa fitar da danyen mai na Najeriya da habaka tattalin arziki, NNPC Ltd ta kaddamar da sabon nau’in danyen mai mai suna Utapate Crude Oil Blend a kasuwar duniya.
A watan Yuli 2024 ne NNPC Ltd tare da hadin gwiwar kamfanin Sterling Oil Exploration & Energy Production Company (SEEPCO) Ltd suka gabatar da Utapate crude oil blend bayan jigilar ganga 950,000 na farko zuwa kasar Spain.
Da yake jawabi a taron Argus European Crude Conference da aka gudanar a birnin Landan, Babban Daraktan NNPC E&P Ltd (NEPL), Mista Nicholas Foucart, ya bayyana cewa kaddamar da Utapate crude oil blend muhimmin ci gaba ne ga fitar da man fetur na Najeriya zuwa kasuwannin duniya.
“Tun da muka fara hakar man a gonar Utapate a watan Mayun 2024, mun samu nasarar kaiwa matakin samar da ganga 40,000 a kowace rana tare da karancin tsaiko. Mun riga mun fitar da jiragen ruwa biyar zuwa Spain da yankin gabashin Amurka, yayin da ake shirin jigilar karin jirage biyu zuwa kasuwannin duniya a watan Nuwamba da Disamba 2024,” in ji Foucart.
Ya kara da cewa, danyen mai na Utapate ya samu karbuwa sosai a kasuwar duniya saboda kyawansa irin wanda ake bukata a masana'antar tace mai.
A cewar Foucart, rukunin hakar mai na OML 13, wanda NEPL da Natural Oilfield Services Ltd (NOSL) ke gudanarwa, yana da arzikin ganga miliyan 330 na danyen mai, miliyan 45 na condensate, da kuma cubic tiriliyan 3.5 na iskar gas.
“Mun tsara kara yawan hakar mai daga ganga 40,000 zuwa ganga 50,000 a rana nan da watan Janairu 2025, sannan zuwa ganga 80,000 a karshen 2025,” Foucart ya bayyana.
A nasa bangaren, Babban Daraktan NNPC Trading Ltd, Mista Lawal Sade, ya ce Utapate crude oil blend na dauke da sinadarai irin na Amenam crude, wanda yake da sinadarin sulphur mai karanci da kuma ingancin samar da man fetur mai daraja.
Ya bayyana cewa NNPC Trading Ltd tana shirin kafa tsari mai dorewa na jigilar Utapate zuwa ga manyan abokan cinikin kasashen Turai da gabashin Amurka.
An samar da man Utapate daga gonar mai ta OML 13 da ke jihar Akwa Ibom, wanda ke da kankantar sinadarin sulphur (0.0655%) da kuma tasirin muhalli mai sauki, lamarin da ya dace da bukatun kasashen Turai.
Wannan nasara ta zo ne kasa da shekara guda bayan kaddamar da man Nembe daga hadin gwiwar NNPC da Aiteo a OML 29. Wannan ya kara tabbatar da himmar NNPC Ltd na bunkasa albarkatun man fetur da arzikin kasa ta hanyar ci gaban sabbin gonakin mai.