TARIHIN SARAUTAR AJIYA A MASARAUTAR KATSINA.
- Katsina City News
- 20 Nov, 2024
- 280
Idan zaa bada Tarihin wata Sarauta a Masarautar Katsina to dole ne a tuna da Sarkin Katsina Muhammadu Korau (1348-1398), saboda shine Sarki na farko daya Fara kawo Tsarin Sarautu a Masarautar Katsina. Sarkin Katsina Muhammadu Korau shine Sarkin Katsina Musulmi na farko, shine kuma ya gina Gidan Sarautar Katsina Wanda yanzu Sarakunan Katsina suke amfani dashi Wanda ke a cikin Unguwar Kofar soro, Wanda ake cema Gidan Korau. Korau ya shinfida Tsarin Sarauta a Katsina. Daga cikin Tsarin Sarautun daya Kawo akwai Sarautar Ajiya. Sarautar Ajiya tana daya daga cikin Tsarin Sarautu na Buwarorin Sarki a wancan Lokacin.
Babban aikin Ajiya shine.
1. Ajine kudin da aka Tara na Kasuwa da sauransu.
2. Ajiye Abincin Gidan Sarki, Wanda aka noma kamar Gero da Dawa, da Masara da sauransu. Da sauransu.
Tun lokacin Sarakunan Habe anyi Ajiya da dama a Masarautar Katsina, Amma ba zaa iya tantance sunayen wadanda suka riki wannan Sarautar a wancan Lokacin ba.
Amma a lokacin Sarkin Katsina Muhammadu Dikko, akwai aminnan shi da suka zauna na anan Kofar soro, a wata Unguwa da ake cema Unguwar Kuka, to daga cikin sune shi Sarkin Katsina Muhammadu Dikko ya nada Sarautar Ajiya.
1. Mutum na farko da aka Fara nadawa shine Ajiya Danladi. Ajiya Danladi aminin Sarkin Katsina Muhammadu Dikko ne, tun ma kamin Sarki Dikkon ya Zama Sarki, tun Sarki Dikko yana Durbi a Kasar Mani. Tarihi ya nuna shi Ajiya Danladi mutumin wani Kauye ne Mai suna Yalli, acikin Kasar Mani. Lokacin da Sarkin Katsina Muhammadu Dikko ya samu Sarauta acikin shekarar 1906, sai shi Ajiya Danladin ya dawo cikin gida Kofar soro da Zama a inda ya zauna a Unguwar Kuka, daga baya Sarkin Katsina Muhammadu Dikko ya nadashi Sarautar Ajiyan Katsina.
Daga cikin zuruar Ajiya Danladi akwai,
A. Malam Mamman , Wanda shi babban Malamine na addinin musulunchi, Wanda ya zauna a nan Unguwar Kukan yana karantar da mutane ilimin addinin Musulunchi,
B. Akwai kuma Malam Jibo ko kuma Atija
C. Sai Malam.Abubakar.
2. Bayan rasuwar Ajiya Danladi sai aka nada Ajiya Jibo a matsayin Ajiyan Katsina. Daga Ajjya Jibo, sai
3. Ajiya Abubakar, Wanda Sarkin Katsina Sir Usman Nagogo(1944-1981) ya nadashi.
Daga cikin zuruar Ajiya Abubakar akwai.
1. Alhaji Tukur Abubakar Ajjya shine Mahaifin Justice Sanusi Tukur Ajiya.
2. Akwai Alhaji Amadu Abubakar, ( Tsohon babban Sakatare na gwamnatin Tarayya) kuma yayi Sakataren Majissar Sarkin Katsina.
3. Alhaj Yusuf Abubakar( Yusuf Ulu). ( Former perm. Sec/ Chairman Civil service Commission, Katsina State.
4. Hajiya Hadiza ( Fada) itace Mahaifiyar Ajiyan Soron Katsina watau, Alhaji Bello Abbas Abubakar ( CNA) an nadashi Ajiyan Soron Katsina a ranar Asabar, 9 ga watan Disamba na shekarar 2023.
5. Akwai Hajjya Amina Wanda tayi aure Gidan Badawan Katsina, ta auri Alhaji Lawal Kafinta, shi kuma Alhaji Lawal Kafinta Dan Alhaji Abdullahi Kafintane, shi kuma Abdullahi Kafinta Dan Turaki Ladanne, shi Kuma Turaki Ladan Dan Turaki Agawa ne, Turaki Agawa Dan Muhammadu Dogo ne. Daga cikin Yayan ta akwai. 1. Late E gineer Hamza Lawal, 2. Akwai Alhaji Muntari Lawal Kofar soro, ( Director Katsina State Government 3. Akwai Shuaibu Lawal 4. Alhaji Kabir Lawal Kofar soro( Bursa, School of Health Sciences Katsina State ) da sauransu.
Bayan da Ajiya Abubakar ya rasu, sai Sarautar Ajiya ta fita daga Gidan Ajiya Danladi ta koma Gidan Zuruar Alkali Hambali a Unguwar Alkali inda Mai Martaba Sarkin Katsina Alhaji Dr. Muhammadu Kabir Usman ya nada Alhaji Lamis Shehu Dikko a matsayin Ajiyan Katsina.
Asalin zuruar su Ajiya Lamis Dikko ya faro ne daga Muhammadu Shumo, Shumo Babban Malami, Wanda ya taso da zuruar shi daga Futa Jalon , ya Fara Zama a Sifawa, inda daga nan yayi kaura da jamaar shi gaba daya, zuwa Makurdi ta cikin Katsina, ance kauyen Makurdi a halin yanzu yana nan a wajen Dandagoro kusa da Masallacin Mai Tuwon Garwa, wajen shekara ta 1750. Anan Makurdi ne Shumo ya kafa makarantar Islamiyya, inda ya rika koyarwa.
Daga baya zuruar Shumo dinner suka kafa Unguwar Alkali a Katsina. Daga cikin zuruar Yan Unguwar Alkali akwai 1. Marigayi Grand Khadi Alhaji Muhammad Dodo. 2. Grand Khadi Aminu Ibrahim 3. Akwai Alkali Yusuf Babba, 4. Justice Ummaru Abdullahi. 5. Akwai Ajiyan Katsina Alhaji Lamis Shehu Dikko.
Alhaji Lamis Dikko Tsohon Maaikachin Banki ne, kuma gogaggen Dan Siyasa. Yayi Managing Director na Bankuna da dama a Tarayyar Nigeria. Yayi takarar Senator Katsina ta Tsakiya a karkashin Jamiyyar PDP a shekarar 2015 da sauransu.
Har ya zuwa yanzu Alhaji Lamis Shehu Dikko, shine Ajiyan Katsina.
Alh. Musa Gambo Kofar soro.