Tinubu ya ayyana sunayen mutane 3 a matsayin masu magana da yawunsa
- Katsina City News
- 19 Nov, 2024
- 244
An nada Sunday Dare da Daniel Bwala a matsayin masu magana da yawun shugaban kasa tare da Bayo Onanuga, bisa amincewar Shugaba Bola Tinubu, a sabon sauyi da aka yi a mukkaraban gwamnatin.
Wata sanarwa da Bayo Onanuga, mai baiwa shugaban kasa shawara kan yad labarai , ya fitar a daren Litinin ya bayyana cewa ba za a sake samun mutum daya da ke magana da yawun shugaban kasa ba. Ya kara da cewa daga yanzu, Sunday Dare da Daniel Bwala za su yi aiki tare a ofishin shugaban kasa a matsayin masu magana da yawun shugaban kasa.
Dare, wanda a baya yake matsayin mai baiwa shugaban kasa shawara kan sadarwa da kyautata tunanin al’umma, yanzu yana da sabon matsayi a matsayin mai bai da shawara kan kafafen watsa labarai da sadarwa.
Haka kuma, an bayyana cewa Bwala, wanda aka sanar makon da ya gabata a matsayin mai baiwa shugaban kasa shawara kan kafafen watsa labarai da sadarwa, yanzu an mayar da shi mai baiwa shawara kan sadarwa kan manufofin gwamnati.
Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa wannan sauyi an yi shi ne domin tabbatar da ingantacciyar sadarwa da jituwa kan manufofi, matakai, da harkokin gwamnatin tarayya.