TATSUNIYA: Labarin Talume
- Katsina City News
- 18 Nov, 2024
- 165
Talume da Rawar Baure
Wata rana wata yarinya mai suna Talume ta tafi daji tare da yayyenta mata da sauran kawaye domin cin baure. Bayan sun gama sha, yayyenta suka ce su share hannayensu da goge bakinsu kada su boye baure domin kaiwa gida. Ashe Talume ta boye wani baure domin ta kai wa mahaifiyarta, kuma har dankon bauren da ya saura a hannunta ba ta goge ba; sai ta rika lasa a hanya har suka isa gida.
Da ta kawo bauren ta ba mahaifiyarta, mahaifiyarta ta tambaye ta:
"Yaya kika samo wannan baure mai dadi haka?"
Talume ta ce: "Ni da su yaya muka samo shi a daji."
### Yarjejeniya da Mahaifiya
Bayan wasu kwanaki, Talume da kawayenta sun shirya zuwa biki. Sai ta roki mahaifiyarta ta ba ta aron zannuwanta. Mahaifiyarta ta ce:
"Zan ba ki, amma sai kin samo mini irin bauren nan da kika kawo wancan lokacin."
Talume ta ce: "Zan je daji in nema."
Tattaunawa da Baure
Da ta isa gindin baure, ta rasa yadda za ta yi, sai ta fara waka:
Talume: "Baure, Baure ka ba ni Baure."
Baure: "In ba ki baure, ki kai wa wa?"
Talume: "In kai wa babata."
Baure: "Ta ba ki me?"
Talume: "Ta ba ni kaya."
Baure: "Ki je ina?"
Talume: "In je biki, 'yan mata duk sun tafi, samari duk sun tafi."
Baure ya ce da ita: "Idan kina so, sai kin kawo min kashin shanu."
Tattaunawa da Shanu
Talume ta nufi shanu tana waka:
Talume: "Shanu, Shanu, ku ba ni kashi."
Shanu: "Mu ba ki kashi, ki kai wa wa?"
Talume: "In kai wa Baure."
Shanu: "Ya ba ki me?"
Talume: "Ya ba ni 'ya'ya."
Shanu: "Ki kai wa wa?"
Talume: "In kai wa babata."
Shanu: "Ta ba ki me?"
Talume: "Ta ba ni kaya in je biki, 'yan mata duk sun tafi, samari duk sun tafi."
Shanu suka ce: "Ki kawo mana ciyawa sai mu yi kashi."
Tattaunawa da Ciyawa
Ta nufi ciyawa tana waka:
Talume: "Ciyawa, Ciyawa, ki ba ni ciyawa."
Ciyawa: "In ba ki ciyawa, ki kai wa wa?"
Talume: "In kai wa shanu."
Ciyawa: "Su ba ki me?"
Talume: "Su ba ni kashi."
Ciyawa ta ce: "Debi ruwa ka kawo mini kafin in ba ki."
Tattaunawa da Gulbi
Ta nufi gulbi tana waka:
Talume: "Gulbi, Gulbi, ka ba ni ruwa."
Gulbi: "In ba ki ruwa, ki kai wa wa?"
Talume: "In kai wa ciyawa."
Gulbi:"Ta ba ki me?"
Talume: "Ta ba ni ciyawa."
Gulbi: "Ki kai wa wa?"
Talume: "In kai wa shanu."
Gulbi ya ce: "Zo ki debi ruwa."
Nasarar Talume
Da ta dawo, ta ba ciyawa, ta yanka ta kai wa shanu. Shanu suka yi kashi mai kyau, sai ta dauka ta kai wa baure. Baure ya ba ta 'ya'yan baure masu yawa. Ta kai wa mahaifiyarta ta ba ta kayan da take bukata, ta shirya ta je biki.
Kiyayya da Dangi
Lokacin da ta je biki, an gama biki. Da kuraye suka gan ta, suka yi kanta za su cinye ta. Ta gudu har gida, amma iyayenta da yayyenta ba su bude mata kofa ba. Daga karshe kakarta ta bude mata ta tsira.
Rayuwar Talume
Washe-gari Talume ta bar garinsu saboda bacin rai. Ta je wani gari, ta yi aure, ba ta sake dawowa ba har iyayenta suka rasu. Sai dai kakarta ce ta rasu, wanda ya sa ta dawo gida domin yi mata addu'a. Sannan ta koma garin mijinta, ta ci gaba da rayuwarta.
Kurunkus.
Daga Littafin Taskar Tatsuniyoyi Na Dakta Bukar Usman