YAN BINDIGA SUN KAI HARI TASHAR KADANYA TA BATSARI
- Katsina City News
- 18 Nov, 2024
- 217
@ Katsina Times
Yan bindiga masu satar dabbobi da garkuwa da mutane domin karɓar kudin fansa, sun kai hari garin Tashar Kadanya dake cikin yankin ƙaramar hukumar Batsari ta jahar Katsina.
Lamarin ya faru ranar lahadi 17-11-2024 da misalin 01:30am na dare, inda suka sadada, suka kwashi mutane bakwai (7), mata hudu, yaran goye biyu da magidanci daya.
Sannan sun harbi mutane biyu, yayinda suke kokarin kubutar da wadanda akayi garkuwa da su, amma hakar su bata cimma ruwa ba.
Matsalar tsaro a wannan yanki ba bakuwa bace domin ko a satin da ya gabata, barayin sunkai irin wannan hari a garin Ɗan Alhaji wacce ke kusa daTashar Kadanya, inda suka dauki mutane 25, kuma har yanzu basu dawo ba.