GWAMNA LAWAL YA RANTSAR DA SABBIN SHUGABANNIN ƘANANAN HUKUMOMI 14, YA BUƘACI SU YI AIKI TUƘURU CIKIN ADALCI
- Katsina City News
- 17 Nov, 2024
- 239
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya buƙaci sababbin zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomin jihar da su bai wa al’ummarsu fifiko wajen tabbatar da adalci a gudanar da ayyukan raya jihar.
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Zamfara (ZASIEC) ta bayyana ’yan takarar jam’iyyar PDP mai mulki a matsayin waɗanda suka lashe zaɓen dukkan kujerun shugabannin ƙananan hukumomi da na kansiloli da aka gudanar a faɗin jihar a ranar Asabar.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa an rantsar da zaɓaɓɓun shugabannin ne a yau Lahadi ta hannun Alƙalin Alƙalan Jihar Zamfara, Mai Shari’a Kulu Aliyu, a tsohon zauren majalisa da ke gidan gwamnati a Gusau.
Sanarwar ta ƙara da cewa, a yayin bikin rantsarwar, Gwamna Lawal ya yaba wa shugabannin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Zamfara (ZASIEC) bisa shirya zabe na gaskiya da adalci.
Gwamnan ya jaddada cewa babban burin tsarin ƙananan hukumomi a Nijeriya shi ne kusantar da gwamnati ga jama'a tun daga tushe.
“Wannan yana da matuƙar muhimmanci a wannan lokaci, domin ƙananan hukumomi, a matsayinsu na mataki na uku na gwamnati, suna da matuƙar muhimmanci wajen ganin an samar da ingantattun ayyukan da gwamnati mai ci ke yi na ceto jihar daga matsalolin da suka shafi zamantakewa da tattalin arziki da kuma matsalolin tsaro da suka addabi sassan jihar.
“Saboda haka, akwai buƙatar haɗin kai tsakanin Majalisun Jihohi da Ƙananan Hukumomi don ƙara habaka cigaba a matakin farko, wanda hakan zai sanya jihar gaba ɗaya ta kasance kan turbar cigaba da wadata.
“Ina kira gare ku da ku kalli zabenku a matsayin kira na yi wa al'umma hidima ta hanyar ba da fifiko ga jin daɗin jama’arku da tabbatar da adalci wajen gudanar da ayyukan raya ƙasa. Kamata ya yi a cimma hakan ta hanyar amfani da shirye-shirye daban-daban na zuba jari da sauran tsare-tsare masu kyau da gwamnati mai ci ta bullo da su domin samar da ayyukan yi ga ɗimbin matasan mu, da samar da su da abubuwa masu amfani, da kuma daƙile aikata munanan laifuka da suka addabi jihar. Za a iya cimma hakan ne kawai idan kun rungumi gaskiya, riƙon amana, da taka-tsantsan wajen sarrafa dukiyar al'umma.
“Dole ne ku haɗa kai da Gwamnatin Jiha, musamman idan aka yi la’akari da tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulkin 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima). Gwamnatin Jiha za ta ci gaba da haɗa kai da kansilolinku domin cimma burinmu tare da samar da haɗin kai don ci gaban jiharmu mai daraja”.
Gwamna Lawal ya kuma buƙaci zababbun shugabannin da su riƙa hulɗa da al’ummarsu yadda ya kamata.
“Ya kamata ku kafa hanyoyin sadarwa masu inganci, waɗanda ke da muhimmanci wajen fahimtar buƙatun mutanen da ku ke yi wa hidima.
“Ya kamata shugabancin ku ya ƙunshi tausayi da haɗa kai da jama'a ta hanyar tabbatar da cewa babu wani bangare na al’umma da aka bari a baya. Ya kamata a ba da kulawa ta musamman ga mutane mafi rauni - mata, yara, masu buƙatu na musamman, da kuma tsofaffi.
“Ina jaddada muku cewa bai kamata ku kebance ayyukanku daga Gwamnatin Jiha ba. Kun kasance wani muhimmin bangare ne na mulki. Don haka, ana sa ran za ku daidaita manufofinku da shirye-shiryenku daidai da abubuwa guda shida na wannan gwamnati: Tsaro, Ilimi, Noma da Tsaron Abinci, Ci gaban Tattalin Arziki, Bangaren Kiwon Lafiya, da Samar da Ababen More Rayuwa.
“A dangane da haka, ya zama wajibi ku ƙirƙiri ɗabi'a ta gaskiya da riƙon amana a dukkan harkokin ku. Ku tabbatar cewa kun adana bayanan kuɗinku da kyau kuma ana duba su lokaci-lokaci. Wannan zai ƙara sahihancin gwamnatocinku, ya kuma sa jama’a su aminta da shugabancinku.”