An Gano Likitocin Bogi 20 A Wani Asibitin Zamfara
- Katsina City News
- 17 Nov, 2024
- 243
Daga Hussaini Yero, Gusau
Shugaban ma’aikatan jihar Zamfara Ahmad Liman, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin tantancewa, tare da aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na Duba Saba'in ya bayyana cewa kwamitinsa ya gano ma’aikatan bogi da dama a cikin jadawalin albashin Zamfara, wanda suka haɗa da Likitocin bogi 20 a wani asibiti a jihar.
Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan shirin gwamnatin Zamfara na aiwatar da mafi ƙarancin albashi na 70,000.
Gwamnati ta kafa kwamitoci da za su tantance haƙiƙanin adadin ma’aikatan jihar da kuma bayar da shawarwari kan sabon tsarin albashin.
Daga nan Ahmad Liman ya jaddada ƙudirin gwamnatin jihar Zamfara na aiwatar da cikakken tsarin mafi ƙarancin albashi da zarar kwamitin ya miƙa rahotonsa a ƙarshen watan nan.
Ya ci gaba da cewa kwamitin na aiki tuƙuru don ganin an yi cikakken aiki da nufin tsaftace alƙaluman lissafin albashin jihar domin aiwatar da albashi yadda ya kamata.
Ya ce, "Kuma Babban ƙalubalen da muke fuskanta shi ne, ana yi wa wasu ma'aikatan aringizon albashi, wasu kuma suna amsar albashi biyu a cikin Jihar."