KWAMITIN TANTANCE MAKARANTUN LAFIYA MASU ZAMAN KANSU....YA CANCANCI YABO DA JINJINA.
- Katsina City News
- 17 Nov, 2024
- 179
Honorable Umar Mammada, mai bawa Gwamnan jihar Katsina shawara akan makarantun lafiya masu zaman kansu
....Ba son zuciya , aiki sukayi tsakani da Allah
...Sharhin jaridun Katsina Times
Kwanakin baya gwamnatin Katsina ta amshi ƙorafin al'umma da aka daɗe ana yi a kan bazuwar makarantun lafiya masu zaman kansu da ba su da ƙwarewa, kuma ba su cika ƙa'ida ba.
Gwamnatin ta kafa Kwamitin karkashin jagorancin Mai baiwa gwamnan Katsina shawara a bangaren makarantun koyon aikin lafiya na jahar Katsina Alhaji Umar Mammada da wasu kwararrun da suka rufa masa baya.
Bincike ya tabbatar da waɗannan makarantun na ta bazuwa kamar wutar daji, kuma suna yaye ɗalibai kamar ya 'ya'yan zomo.
Ɗaliban sun bazu a birane da ƙauyuka suna raba magani da allurai ga mutane, wanda wannan ya sa Allah kaɗai ya san yawan mutanen da aka illata, ko aka salwantar ta waɗannan gurɓatattun ɗalibai.
Misali gidan Rediyon Jamus (DW) ya ba da labarin wani namiji da irin waɗannan ɗalibai suka yi wa allurar naƙudar haihuwa.
Wasu rahotanin sirri sun ce irin waɗannan ɗalibai har daji suke shiga suna yi wa ɓarayin daji magani.
Takardun kammala karatun lafiya na bogi daga irin waɗannan makarantun sun cika Katsina da wasu jihohin maƙwabtan Katsina.
An yi koke a majalisar dokokin jiha, an yi ga jami'an tsaro, an yi ga iyayen ƙasa sarakuna, amma duk ba matakin da aka ɗauka a baya.
Jama'a sun yi farin ciki da jin gwamnatin Katsina ta shelanta kafa Kwamitin da zai tantance waɗannan makarantun ƙarƙashin mai ba gwamnan Katsina shawara a kan makarantun lafiya na jihar Katsina Alhaji Mada.
Kwamitin ya ɗauko membobinsa daga ɓangarori daban-daban da suka san harkar lafiya da tafiyar da makarantun. Sun tsara kansu bisa yadda ilmin kafa irin waɗannan makarantun yake suka kuma kama aiki gadan-gadan.
Kwamitin sun sha alwashin aiki tsakaninsu da Allah da sanin aiki da kuma kishin makarantun da ceto rayuwa ka da lafiya na al'umma.
Kwamitin ya gayyaci duk makarantun lafiya masu zaman kansu, ya kuma kai ziyarar gani da ido ga duk makarantun da suka kawo kansu don tantancewa.
Abin da kwamitin ya riƙa yi, tare da rakiyar 'yan jaridu kowace makaranta za a duba takardunta, za a duba kos ɗin da take koyarwa, sannan a duba malamanta da kuma takardunsu. Za kuma a duba ginin da kayan aikin koyarwar. Za a yi wa mai makarantar ko shugabanta tambayoyi. Sannan sai su wuce makarantar ta gaba.
Duk ana wannan gaban duk 'yan kwamitin da mai makarantar da kuma 'yan jarida na shaida.
A aikin na Kwamitin makarantu 30 suka kawo bayyana kansu. Yayin da sama da 15 suka ki kawo kansu kamar yadda jaridun Katsina Times suka gano
Binciken Katsina Times ya tabbatar ba makarantar lafiya da aka samu da lafiya ɗari bisa ɗari, kowacce akwai gyaran da ke gabanta, akwai kuma kuskuren da take yi.
Kwamitin ya kasa makarantun kashi uku; Kashin farko sune guda takwas. Waɗanda suka cancanta su buɗe su gaba da karatu, amma su ma ga gyaran da za su yi a daidai lokacin da suke karatunsu, kowanne kuma da kos ɗin da aka amince ya koyar.
Sai kuma guda bakwai da aka ba su umurnin su je su yi gyare-gyare su dawo a tabbatar kafin a buɗe su.
Sauran kuma su je Ma'aikatar Lafiya a ilmantar da su yadda ake buɗe irin waɗannan makarantun a ɗora su a kan hanya.
Wani abin burgewa da nuna bin ƙa'idar aiki, wanda Kwamitin ya bi, shi ne sam alfarma ba ta shigo ba.
Daga makarantun da aka kulle har da ta wasu manyan 'yan siyasa, waɗanda ke da tasiri a siyasar Katsina da kuma sanayya a siyasar ƙasar nan, amma sam aiki aka yi na ilmi da ƙa'ida. Tasirin iyasa bai yi amfani ba.
Daga cikin makarantun da aka kulle kwata-kwata aka ce su zo a ilmantar da su ƙa'idar buɗe irin waɗannan makarantun. Akwai masu alaƙa da manyan mutane a jihar da kuma ƙasar, amma duk wannan bai yi amfani ba. Ƙa'ida kawai aka bi in ka cika, to ka haye.
Yadda wannan Kwamitin ya yi aikinsa idan duk Kwamitocin da gwamnatin Katsina za ta riƙa kafawa don gyara, haka za su riƙa aikin su, tabbas jihar Katsina za ta bunƙasa, kuma ta ci gaba.
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai
@ www.katsinatimes.com
All on All social media platforms
07043777779 08057777763