Farashin shinkafa ƴar gida zai karu da kashi 55% a 2025 – Rahoto
- Katsina City News
- 16 Nov, 2024
- 345
Ana sa ran farashin shinkafa da aka noma a gida zai tashi da kimanin kashi 55% a kakar noman 2024/2025, wanda zai kara ta'azzara matsalar tsadar rayuwa, in ji wani sabon rahoto.
Nairametrics ta rawaito cewa rahoton Afex na Noman Damina na 2024, wanda Nairametrics ta samo, ya nuna ci gaba da tashin farashin shinkafa.
Rahoton ya bayyana cewa a kakar 2023/2024, farashin shinkafa ya karu da kashi 78%, inda matsakaicin farashi ya kai Naira 630,000 a kowanne tan na ma'aunin metric.
An alakanta wannan tashin farashin mai tsanani da karancin shinkafa a kasuwa da kuma karuwar bukata, wacce ta zarce adadin da ake da shi a hannun mutane.
Haka zalika, rahoton ya hasashen karin tashin farashi na kimanin kashi 55% a kakar noman gaba.
Ana danganta wannan tashin farashin da tsadar farashin farko na kakar 2024/2025, wanda aka kiyasta zai kai kimanin Naira 750,000 a kowanne tan na ma'aunin metric, yana nuna ci gaba da karancin kayayyaki.
A nan da karshen shekarar 2025, ana hasashen farashin shinkafa zai kara tashi zuwa tsakanin Naira 1,100,000 da Naira 1,300,000 a kowanne tan na ma'aunin metric.