TARIHIN SARAUTAR MAGAYAKIN KATSINA.
- Katsina City News
- 16 Nov, 2024
- 345
Sarautar Magayaki tsohuwar sarautace a Masarautar Katsina,kuma tana daya daga cikin Sarautu na Mayaka, ko kuma kwamandojin yaki a wannan lokacin. Ance an Fara wannan Sarauta ta Magayaki tun lokacin Sarakunan Habe, lokacin Kasar Hausa tana cikin rudun yake yake. Daga cikin Sarautun Yaki a wancan lokacin akwai Sarautar Kaura Wanda shine babban kwamandan Rundunar Yaki, akwai Uban Dawaki, akwai Magayaki, da sauransu.
Sarautar Magayaki tana daya daga cikin manyan Sarautu a Kasar Hausa, shiyyasa ba kowa ake ba Sarautar ba sai Jarumi Wanda jaruntarsa ta bayyana. A Katsina Sarautar Magayaki tana daga cikin tsarin Sarautu na Buwarori da suka hada da Turaki, Magayaki, Sarkin Bai, Ajiya, Tarno, da sauransu. A Katsina tun daga shekarar 1807 har zuwa 1903 zuwan Turawan mulkin Mallaka, Sarautar Magayaki tana daya daga cikin manyan Fadawa masu Fada ajj a fadar Sarkin Katsina.
Tarihi bazai tuna da Magayakin da akaba a lokacin mulkin Habe. Amma a lokacin mulkin Dallazawa zuwa yanzu anyi Magayaki da dama a Katsina. Daga cikin su akwai.
1. Magayakin Katsina Muhammad Gajeran Bade. Shi Gajeran Bade asalinshi mutumin Kasar Bade ne, yazo Katsina a lokacin mulkin Dallazawa, lokacin ana yake yake tsakanin Katsina da Maradi. Yayi Sarautar Sarkin Bai, da Ajiya da sauransu, sai a lokacin Sarkin Katsina Ibrahim aka bashi Sarautar Magayakin Katsina. Daga cikin zuruar Gajeran Bade akwai 1. Marusan Katsina na yanzu 2. Senator Hadi Sirika 3. Alhaji Ahmed Idris Yamel Maje Baden Katsina da sauransu. Har ya zuwa yanzu zuruar Magayaki Gajeran Bade sune suke mulkin Kasar Dutsi.
2. Akwai Magayaki Nasamu. Shi Muhammadu Nasamu asalin shi mutumin Kasar Borno ne( Babarbare) yazo Katsina a lokacin mulkin Dallazawa. Yayi Sarautar Dankafin Katsina, Ajiya, da Sarkin Bai. Daga baya aka nadashi Sarautar Magayaki. Daga cikin zuruar Magayaki Nasamu akwai. 1. Late Alhaji Bello Kofar Bai 2. Justice Aminu Tukur Kofar Bai 3. Alhji Aminu Bello Kofar Bai Magayakin Katsina. Da sauransu.
3. MAGAYAKI KWALALE.
Muhammadu Kwalale an haifeshi a shekarar 1834 a wani gari Mai suna Auyo dake cikin Masarautar Hadejia ta yanzu. Amma asalin Kakannin shi mutanen Borno ne.
Muhammadu Kwalale yazo Katsina a karshen mulkin Dallazawa. An nada Muhammadu Kwalale Sarautar Magayakin Katsina a cikin shekarar 1887, lokacin mulkin Sarkin Katsina Abubakar, ya rike wannan Sarautar har zuwa lokacin Sarkin Katsina Muhammad Dikko 1907. Daga cikin zuruar Magayaki Kwalale akwai 1. Late Alhaji Ummaru Kadarko 2. Akwai Shanaki Ammani 3. Akwai, Alhaji Saidu Barda ( Tsohon Gwamnan Jihar Katsina da sauransu.
Alh. Musa Gambo Kofar soro.