Babbar Mota Dauke Da Iskar Gas Ta Kama Da Wuta a Jibia, Jihar Katsina, Motoci Shida Sun Lalace
- Katsina City News
- 15 Nov, 2024
- 264
Zaharaddeen Ishaq Abubakar (Katsina Times)
Hukumar ’Yan Sandan Jihar Katsina ta tabbatar da wata mummunar gobara da ta auku a safiyar yau, 15 ga Nuwamba, 2024, a kusa da gidan mai na Tamal, karamar hukumar Jibia. Gobarar ta auku ne bayan wata babbar mota dauke da tankunan iskar gas ta kama da wuta, lamarin da ya jawo asarar dukiya mai yawa.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 8:45 na safe. A cewarsa, bayan jin karar fashewa, DPO na rundunar a Jibia ya jagoranci tawagar jami'an tsaro tare da hadin gwiwar sojoji zuwa wurin domin daukar matakin gaggawa.
Bayan isarsu, jami’an tsaron sun tarar da babbar motar dauke da tankunan iskar gas tana cin wuta a gidan mai na Tamal, da ke kan hanyar Kagadama zuwa Magamar Jibia. Tuni tawagar hadin gwiwar ta yi nasarar kashe wutar, tare da rage yuwuwar karin asara.
ASP Abubakar ya tabbatar da cewa motoci guda shida sun lalace sakamakon wannan ibtila’i, amma babu asarar rayuka da aka samu.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Katsina, CP Aliyu Abubakar Musa, ya bayar da umarnin gudanar da bincike mai zurfi domin gano musabbabin tashin gobarar. Rundunar ta kuma yi alkawarin sanar da ci gaban binciken a nan gaba.