Makarantun Kiwon Lafiya Masu Zaman Kansu Takwas Kadai Suka Samu Izinin Cigaba Da Aiki A jihar Katsina ...an Rufe 14 Saboda rashin cika Ƙa'idoji
- Katsina City News
- 14 Nov, 2024
- 536
Zaharaddeen Ishaq Abubakar (Katsina Times)
A wani taron manema labarai da ya gudana ranar Alhamis 14 ga watan Nuwamba 2024, A ofishin Mai bawa Gwamnan jihar Katsina Shawara akan Cibiyoyin Lafiya Honorabul Umar Mammada, ya sanar da sakamakon binciken da aka yi wa makarantun koyar da Ilimin lafiya masu zaman kansu a jihar. An raba makarantun zuwa rukuni uku bisa ga cika ka’idojin gwamnati: wadanda suka cika ka’idoji gaba ɗaya, wadanda suka cika wasu ka’idoji, da kuma wadanda suka gaza cikawa kuma aka umarci su rufe a nan take.
Makarantu takwas aka tantance kuma sun cika dukkan ka’idojin da ake bukata, an basu izinin ci gaba da gudanar da ayyukansu. Makarantun sun hada da:
1. ESS EMM College of Nursing Sciences
2. Bawo College of Nursing Sciences
3. Cherish College of Nursing
4. Northwest College of Nursing Sciences
5. Muslim Community College of Health Science and Technology
6. Cherish College of Health Science and Technology
7. Khuddam School of Health Technology
8. Cognate School of Health Technology
Waɗannan makarantun za su ci gaba da aiki tare da wasu gyare-gyare na kananan matsaloli.
Makarantun da Ba Su Cika Ka’idoji Gaba Daya Ba
An gano cewa akwai wasu makarantun bakwai da suke da wasu ƙananan gibobi wajen cika ka’idoji, kuma an shawarce su da su cike waɗannan gibobin kafin su sake fara ayyukansu. Makarantun sun hada da:
1. Alliance College of Public and Environmental Health
2. Global College of Health Science and Technology
3. GIAL College of Health Science and Technology and Environmental Science
4. Kebram College of Health Science and Technology
5. Barda College of Health Science and Technology
6. Funtua Community College of Health Science and Technology
7. College of Health and Environmental Sciences
Makarantun da Aka Rufe Saboda Rashin Cika Ka’idoji
Makarantu goma sha hudu an gano cewa ba su cika ka’idojin da ake bukata ba, musamman wajen takardar izinin koyarwa, gina wuraren karatu, ingancin malamai, da tsarin koyarwa. Wadannan makarantu sun hada da:
1. Health Careers Academy School of Health Technology, Jibia
2. Superb College of Health Science and Technology, Jibia
3. Katsina College of Health Science and Technology Limited
4. Rabe Abdullah College of Health Science and Technology
5. Al-Azhar School of Health Science and Technology
6. Umar Bin Umar Bin Khattab College of Health Science and Technology
7. MS Abubakar College of Health Science and Technology
8. Halima Adamu School of Health Technology, Malumfashi
9. Empirical School of Health Science and Technology
10. Kingdom College of Health Science and Technology
11. Umar Farooq Bilingual College of Nursing Sciences, Daura
12. Katman School of Health Technology, Daura
13. Alkalam University Katsina Consultancy Services
14. Kingdom College of Health Science and Technology
Gwamnati ta bayyana cewa rashin cika muhimman ka’idoji, irin su izinin koyarwa, gina wuraren da suka dace, cancantar malamai, da tsarin koyarwa, su ne manyan dalilan da suka sa aka rufe waɗannan makarantu. Bugu da ƙari, wasu makarantu sun gaza samun lasisin koyarwa da ake bukata don su ci gaba da aiki a matsayin cibiyoyin koyar da lafiya.
Mammada ya tabbatar da cewa gwamnati na duba hanyoyin da za a tallafa wa daliban da abin ya shafa, domin su ci gaba da karatunsu ba tare da wata matsala ba. Za a ci gaba da sanar da dalibai da al'umma a kan matsayin kowacce makaranta lokaci zuwa lokaci.
Wannan matakin na nuni da jajircewar Gwamnatin Jihar Katsina wajen tabbatar da ingancin ilimin kiwon lafiya, domin samar da kwararrun jami’an lafiya masu nagarta da za su iya bauta wa al’ummar jihar da ƙasa baki ɗaya.