Katsina Ta Amshi Bakuncin Taron Manyan Yan Kasuwa Da Ƙanana don Bunkasa Kasuwanci a Shiyyar Arewa Maso Yamma
- Katsina City News
- 12 Nov, 2024
- 178
Zaharaddeen Ishaq Abubakar (Katsina Times)
A jihar Katsina, an fara gudanar da wani taro mai taken "PEBEC Subnational Tour Northwest Region," wanda ke da nufin bunkasa kasuwanci a shiyyar Arewa maso Yamma ta hanyar hadin gwiwa tsakanin yan kasuwa, shugabanni, da masu ruwa da tsaki. Wannan taron wanda gwamnatin jihar Katsina ke masaukinsa, ya soma ne a ranar Talata, 12 ga watan Nuwamba, kuma ana sa ran za a kammala shi ranar Alhamis, 14 ga watan Nuwamba.
Taron ya samu halartar yan kasuwa daga dukkan jihohin yankin Arewa maso Yamma, ciki har da kamfanoni da kananan yan kasuwa daga jihohin Jigawa, Kebbi, Zamfara, Sokoto, Kano, Kaduna, da jihar Katsina. Manufar wannan taro ita ce tattaunawa kan kalubalen da yan kasuwa ke fuskanta, da gano hanyoyin da za a magance su domin habaka kasuwanci da ci gaban tattalin arziki a yankin Arewa maso Yamma.
A Babban Dakin Taro na Sakatariyar gwamnatin jihar Katsina ake gudanar da taron, inda Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, wanda mataimakinsa Alhaji Faruq Lawal Jobe ya wakilta, ya kasance cikin manyan baki. Haka zalika, gwamnonin Kano, Jigawa, Kebbi, Zamfara, Sokoto da Kaduna, duk sun samu wakilci a wannan taro, suna tabbatar da goyon bayansu ga shirin bunkasa kasuwancin yankin.
Ana sa ran wannan taron zai kawo sauyi mai ma'ana ga fannin kasuwanci da tattalin arzikin Arewa maso Yamma, tare da samar da hadin kai da haɗin gwiwa tsakanin yan kasuwa da gwamnatoci wajen inganta yanayin kasuwanci, samar da aikin yi, da rage radadin talauci a yankin.