BARAYIN DAJI SUN SACE MUTANE 32 A YANKIN BATSARI
- Katsina City News
- 12 Nov, 2024
- 212
Ahmad Muhammad daga Batsari - Katsina Times
Barayin daji sun yi garkuwa da mutane 32 a yankin Batsari na jihar Katsina.
Lamarin ya faru a daren Asabar, 9 ga Nuwamba, 2024, a garuruwan Dan'alhaji da Maidoriya.
Rahotanni sun nuna cewa barayin sun afka kauyen Maidoriya inda suka bindige mutane biyu, sannan suka sace mutane bakwai, ciki har da mata shida da namiji daya.
A kauyen Dan'alhaji, barayin sun dauki mutane 25, yawancinsu mata da kananan yara. Mutane da ‘yan uwan wadanda abin ya shafa sun tabbatar da wannan labari ga jaridar Katsina Times.
Harin dai ba sabon abu ba ne ga mazauna yankin, domin a kwanakin baya ma an samu rahoton sace mutane a kauyen Gaje, wanda ke kusa da Maidoriya.
Mun yi kokarin jin ta bakin jami’an tsaro dangane da lamarin, amma bamu samu nasara ba.
**Katsina Times**
@ www.katsinatimes.com
**Jaridar Taskar Labarai**
@ www.taskarlabarai.com