UNGUWAR SARARIN KUKA KATSINA.
- Katsina City News
- 11 Nov, 2024
- 231
Unguwar Sararin Kuka dake cikin Birnin Katsina ta samo sunantane daga wasu Kukoki dake a Kofar Gidan Kankia Ummaru. Wadannan Kukeki guda akwai wani Katon Dutsi dake a wurin su, ance anan Kankia Ummaru yake hutawa tare da mutanensa a wannan Dutsen, to daga sunan Sararin Kuka ya samo asali.
Unguwar Sararin Kuka wani bangarene daga cikin Unguwannin Sansanin Yan Sarki na Dallazawa da suka hada da Unguwar Yari, Unguwar Madawaki, Unguwar Alkali, Unguwar Yarima Adoro da ita kanta Sararin Kukar. Unguwar Sararin Kuka daga Arewa maso Gabas tayi iyaka da Unguwar Madawaki. Daga kudu-maso Gabas ta yi iyaka da Unguwar Yarima. Daga Yamma ta yi iyaka da Yanshuni. Sannan daga Arewa ta yi iyaka da Unguwar Yari.
ASALIN wurin da unguwar Sararin Kuka take Gandu na Sarkin Katsina Ummarun Dallaje. Da can ana Kiran wurin Gandun Sarki. Watau Gandu ne na Sarakunan Dallazawa inda suke nomawa, watau tayi Kama da Gandun Dallzawa na kauyen Tarkama, sai dai shi Gandu dake Sararin Kuka iyakar zuruar Sarkin Katsina Muhammadu.Bello ne suke noma shi.
Unguwar Sararin Kuka ta Tara mashahuran Mutane da suka da
1. Kankia Ummaru Dan Sarkin Katsina Abubakar.
Gidan Kankia Ummaru shine yanzu akayi Makarantar Firamare ta Sararin Kuka da Asibitin Jariri. N. A ta Katsina ta fanshi wajen wajen zuruarshi bayan rasuwar shi. Ance an Gina Sararin Kuka Firamare da Asibitin Jarirai a shekarar 1965. Yanzu haka Kabarin Kankia Ummarun Yana nan a cikin harabar Sararin Kuka Firamare, wannan al'adace ta Sarakunan da, idan sun rasu yawanci a gidajensu ake rufesu.
Yanzu wannan Firamare an canza Mata suna daga Sararin Kuka Firamare zuwa Ummarun Dallaje Firamare School.
Gidan Yana Kallon kusurwar Yamma ta wajen Gidan Sa'i, kusa da wajen akwai wasu gidajen Dallazawa kamar haka.
1. Gidan Dan Yusufa Yahaya. Ita wannan Sarauta ta Danyusufa Tsohuwar Sarautace tun Habe, ance wani mutum Mai suna Yusufa, Wanda ya fito daga Kasar Kamri, ta Bindawa shine mutum na farko daya Fara mulkin Garin Bindawa, bayan rasuwarsa Sai wani dansa ya gaji Sarautar Dagacin Bindawa, to tun daga wannan lokacin aka rika kiranshi Dan Yusufa. Da Dallazawa suka amshi mulki Sai suka maida Sarautar a matsayin Hakimi, watau Dan Yusufan Katsina Hakimin Bindawa. Har ya zuwa yanzu dai Dallazawa ke mulkin Kasar Bindawa da sunan .Sarautar Dan Yusufan.
2. Akwai Kuma Gidan Lambisa Abdulmumini.
Lambisa sunan Sarauratace a Gidan Dallazawa. ASALIN sunan Tabkin Lambusu kenan, Wanda yanzu aka cike akayi Islamiyya a wurin.
Baya ga Zuruar Dallazawa akwai sauran manyan Gidajen dake Unguwar Sararin Kuka kamar:---
1. Gidan Sarkin Daura. Shi wannan Gida asalinshi masabkine na duk Wanda ya kasance shine Sarkin Daura. Kamar yadda aka Gina Gidan Sarkin Kano a Yar'adua.
2. Akwai Gidan Malam Barmo. Shi wannan Malam Barmo Yana daya daga cikin manyan Malamai masu bada shawara a Fada lokacin Sarkin Katsina Muhammadu Dikko, shine kuma limamin Jumaa na Masallacin Kofar Kaura. Sannan Yana daya daga cikin tawagar da suka yi aikin Hajji na farko da Sarkin Katsina Muhammad Dikko.a shekarar 1921.
3. Akwai Kuma Gidan Malam Jibril Alkali, mahaifin Dr. Lema Jibril.
4. Akwai Kuma Gidan Sain Katsina Alhaji Ahmadu Na Funtua, Wanda aka nada Sarautar Sai tun Lokacin Sarkin Katsina Alhaji Sir Usman Nagogo (1944-1981).
Ita wannan Sarauta ta Sai ta samo asalintane daga Kalmar Larabci watau Abinda ake nufi da Sai shine Mudannabi watau abin awon Hatsi. Yawancin Daulolin Musulunci irinsu Daular Turkiyya da Daular Usmaniyya ta Sokoto duk suna da wannan Sarauta ta Sai. Babban aikin mai rike da wannan Sarautar shine. 1. Tattarawa da raba zakka ga wadanda suka dace. 2. Ba Sarki Shawara akan yadda zaa taimakawa Talakawa. 3. Tabbatar da ansa da raba Zakka yadda Sharia ta tanada da sauransu.
5. Akwai Gidan Alhaji Abba 33 Dan uman Sain Katsina Alhaji Ahmadu na Funtua.
6. Gidan Musan Gani. Dan Alhaji wani babban dan Kasuwa na Yanshuni.
7. Akwai Gidan Alhaji Armayau na Yan Serelean
8. BBC
9. Alh. Babba driver da sauransu.
A wannan Unguwa anyi wasu Tabkuna wadanda sukayi suna kwarai a Birnin Katsina, irinsu Tabkin Lambusu, da Tabkin Ci Rakumma da Tabkin Nababa da Tabkin Mai Koko.
An Kuma yi makadan Fada a Sararin Kuka irinsu. 1. Sarkin Makada Danmai Waina. 2. Sarkin Makada Ali. 3. Sarkin Makada Abu Gagare da sauransu. Har yanzu zuruar wadannan Makada sunan a Sararin Kuka.
Alhaji Musa Gambo Kofar soro.