Sakamakon damfarar matan Amurka dala miliyan 3.3, FBI ta cafke ciyaman din ƙaramar hukumar Anambra
- Katsina City News
- 09 Nov, 2024
- 153
An kama wani sabon zababben shugaban karamar hukumar Ogbaru ta jihar Anambra, Franklin Nwadialo, a jihar Texas ta Amurka, bisa zarginsa da damfarar mata da sunan soyayya har dala miliyan 3.3.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na yanar gizo a ranar Talata, ma'aikatar shari'a ta Amurka ta sanar da cewa hukumar bincike ta kasa, FBI, ta kama ciyaman din mai shekaru 40 a lokacin da ya sauka a birnin Texas.
Ma'aikatar ta bayyana cewa za a mika Nwadialo zuwa yankin yammacin Washington domin gurfanar da shi a gaban kuliya, inda ta kara da cewa ya na fuskantar tuhume-tuhume 14 kuma zai iya fuskantar hukuncin daurin shekaru 20 idan aka same shi da laifi.
Ta bayyana cewa wanda ake tuhumar ya yi amfani da hotunan karya a cikin bayanansa kuma ya damfari mata kudade da sunan soyayya.