Gwamnatin jihar Katsina ta sake Kaddamar da Jami'an tsaron Kwaminiti karo na biyu don inganta tsaron al'umma
- Katsina City News
- 08 Nov, 2024
- 16
Auwal Isah, Zaharaddeen Ishaq Abubakar (Katsina Times)
A ranar Jumma’a, 08 ga Nuwamba, 2024, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Radda, Ph.D., CON, ya kaddamar da sabbin jami’an tsaro na al’umma mutum 555 da aka zabo daga kananan hukumomi goma a jihar. An zabo wadannan jami’an ne daga Bakori, Danja, Dutsinma, Kurfi, Kafur, Matazu, Charanchi, Musawa, Malumfashi, da Funtua, kuma za su taimaka wajen samar da tsaro a yankunansu.
Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Radda ya jaddada muhimmancin hadin kan al’umma wajen samar da tsaro. Ya tunatar da cewa a bara an tura irin wadannan jami’an mutum 1,466, kuma hakan ya kawo gagarumar sauyi a fannin tsaro a jihar. “Ta hanyar hadin gwiwar wadannan jami’ai tare da sauran hukumomin tsaro da goyon bayan al’umma, Jihar Katsina ta ga kyakkyawar nasara a harkar tsaro,” inji shi.
Gwamna Radda ya bayyana cewa samar da tsaro ba hakkin gwamnati kadai ba ne, hakki ne na kowa, kuma ya yi kira ga al’umma da su taimaka wa jami’an tsaro don tabbatar da zaman lafiya mai dorewa. “Zaman lafiyar Jihar Katsina hakki ne da ya rataya a kan kowane dan jihar. Saboda haka, ya zama wajibi mu ba wadannan jami’ai goyon baya don tabbatar da zaman lafiya da kare mutunci da dukiyoyin al’umma,” ya bayyana.
Gwamnan ya kuma nuna irin amfanin wannan shiri na tsaro, inda ya ce ya samar da kimanin kashi 90% na tsaro ga manoma, wanda ya basu damar yin noma da kwashe amfanin gonakinsu ba tare da tsoro ba. Ya gode wa al’ummar Katsina da hukumomin tsaro kan hadin kai da goyon bayan da suka bayar, wanda hakan ya taimaka wajen samun wannan nasara mai mahimmanci.
Shi ma da yake jawabi na maraba, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Jihar Katsina, Dakta Nasiru Ma’azu Danmusa, ya yaba wa Gwamna Radda bisa goyon bayan da yake ba wa ma’aikatar, wanda ya zama ginshiki wajen tabbatar da tsaro a fadin jihar.
Bikin kaddamarwar ya gudana ne a Kwalejin Horas da Jami’an Tsaron Farin Kaya da ke Katsina, kuma ya samu halartar Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina, Hon. Faruk Lawal Jobe; Kakakin Majalisar Dokokin Jihar, Rt. Nasir Yahaya Daura; ‘yan majalisar dokoki; Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Katsina, Alh. Jabiru Salisu Abdullahi Tsauri (Lamidon Katsina); da wasu manyan sarakuna da shugabanni daban-daban.
Sabbin jami’an tsaron al’umma da aka kaddamar, wanda aka fi sani da “Katsina Community Watch Courps,” (KCWC) sun samu kayan aiki kamar motocin hawa, babura, da makamai domin gudanar da aikinsu na kare rayuka da dukiyoyin al’umma a yankunansu.