Kwamitin Tantance Makarantun Kiwon Lafiya masu Zaman Kansu a Katsina Na Ci Gaba da Ziyarar Gani da Ido Don Inganta Ingancin Ilimi
- Katsina City News
- 01 Nov, 2024
- 436
Daga Muhammad Aliy Hafiziy
A ranar Alhamis, 31 ga Oktoba, 2024, Kwamitin Tantance Makarantun Kiwon Lafiya masu zaman kansu da aka dakatar a Jihar Katsina ya ci gaba da ziyarar gani da ido a makarantu daban-daban, karkashin jagorancin mai ba Gwamna shawara akan Cibiyoyin kiwon lafiya, Alhaji Umar Mammada.
Wannan kwamiti da Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, ya kafa na da nufin tabbatar da cika dukkan ka'idoji kafin makarantun da aka dakatar su koma bakin aiki.
Kwamitin ya kai ziyara ga wasu daga cikin manyan makarantun kiwon lafiya a jihar, ciki har da Bawo College of Nursing Science Daura, Gial College of Health Technology and Environmental Sciences, Khuddam College of Health Science and Technology, da Cherish College of Health Sciences Batsari. Manufar ziyarar ita ce a tantance ingancin kayan koyarwa, adadin malaman da suka dace da fannin da ake koyarwa, cika ka'idoji na ilimi, dakunan gwaje-gwaje da na nazari, da kuma yawan azuzuwa da yanayin gudanar da karatun dalibai.
A yayin wannan ziyara, shugaban kwamitin, Alhaji Umar Mammada, ya bayyana cewa, “Kamar yadda kuka sani, satin da ya gabata kun kawo takardun bayanai na makarantunku zuwa Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Katsina domin tantance ko kun cika ka'idoji. Wannan shi ne dalilin da yasa muka kawo ziyara a yau domin gani da ido da tabbatar da sahihancin bayanan da kuka gabatar."
Shugabannin makarantun da aka ziyarta sun nuna jin dadinsu ga wannan mataki na gwamnatin jihar na tabbatar da ingancin ilimi da tsare-tsaren kiwon lafiya. Sun yaba wa gwamnatin bisa ƙoƙarin da take na ganin makarantun da suka cika ka'ida sun dawo bakin aiki, yayin da kuma ake tabbatar da ingantattun tsare-tsare don cigaba da bunkasa harkan kiwon lafiya a jihar Katsina baki daya.