Yanda Za'a gudanar da Zagayen Maulidin jihar Katsina
- Katsina City News
- 10 Sep, 2023
- 1033
KHATMAR MIFTAHUL-MAWLUD: A JIHAR KATSINA
An bayyana ranakun zagayen Mauludi na jihar Katsina....
Mataimakin Shugaban babban ƙwamitin zagayen Mauludi na Jihar Katsina, Sheikh Haruna Bakin-gida, ya sanar da ranaikun zagayen Mauludin jihar Katsina na wannan shekara, kamar haka;
1. Zagayen farko na ƴan Islamiyyu, zai kasance ranar Lahadi, 8/October/2023.
2. Zagayen Gidan Sheriff Abba Abu, zai kasance ranar Litinin, 9/October/2023.
3. Za'a Gabatar da Mauludin Jiha, a ƙaramar Batagarawa, ranar Asabar, 14/October/2023.
4. Sai Babban zagaye na gari duka, ranar Lahadi, 15/October/2023. In shaa Allahu!
Dan Allah a kiyaye lokacin fita da kammala zagaye, daga ƙarfe Takwas 8am na safe, zuwa ƙarfe Shidda 6pm na yamma.
Da fatan, Allah Ya kaimu lokacin lafiya, Ya sanya ayi lafiya, a gama lafiya, Alfarmar Annabi Muhammadu ﷺ Amin.
Happy Maulud