Jami'ar Tarayya Dutsinma Zata Yi Bikin Yaye Ɗalibai Karo na Tara
- Katsina City News
- 30 Oct, 2024
- 237
Zaharaddeen Ishaq Abubakar (Katsina Times)
Mataimakin Shugaban Jami’ar Tarayya Dutsinma (FUDMA), Farfesa Armaya'u Hamisu Bichi, ya gudanar da taron manema labarai a ranar Laraba, 30 ga Oktoba, 2024, a dakin taro na jami’ar, inda ya yi bayani kan shirye-shiryen bikin yaye dalibai karo na tara da jami’ar za ta gudanar a ranakun 1 da 2 ga Nuwamba, 2024.
Farfesa Bichi ya bayyana cewa, "A ranar Juma'a, 1 ga Nuwamba, za a fara da gabatar da jawabi na musamman daga bakin Mai Girma Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani." Bayan haka, za a shirya babbar liyafar shugaban jami’ar wanda za a gudanar a garin Katsina.
A ranar Asabar, 2 ga Nuwamba da misalin karfe 10 na safe, za a fara babban taron yaye dalibai na gama gari, inda za a karrama dalibai guda 307 da suka kammala karatun digiri na biyu, wadanda suka hada da digiri na masters da PhD. Baya ga haka, za a yaye dalibai 4,588 da suka kammala digirin farko, ciki har da sama da 100 masu karatun digiri biyu.
Haka kuma, jami'ar za ta karrama wasu fitattun 'yan Najeriya guda hudu saboda gudunmawar da suka bayar wajen cigaban kasa. Wadannan manyan mutane sun hada da Mai Girma Sanata Remi Tinubu, matar Shugaban Kasa, saboda kyakkyawar jagorancinta da goyon bayanta wajen inganta ilimin ‘ya’ya mata. Lokacin da aka sace wasu dalibai mata guda biyar, ta taka rawar gani wajen ganin an kubutar da su tare da ba su tallafin karatu har zuwa matakin da suke yanzu.
Mai Girma Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, shi ma za a karrama shi da digiri na girmamawa a fannin kimiyyar siyasa saboda kokarinsa wajen cigaban jami'ar da kuma shugabanci na gari a majalisa.
Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, tsohon gwamnan jihar Sakkwato wanda yanzu shine shugaban kwamitin tsaro na majalisar dattawa, zai samu digiri na girmamawa saboda jajircewarsa wajen inganta harkokin tsaro a yankin arewa maso yamma da kuma tallafa wa jami’ar ta fuskar ci gaba.
Kazalika, za a karrama Hon. Abubakar Kabir Abubakar, shugaban kwamitin kasafin kudin majalisar wakilai, saboda goyon bayansa ga harkokin ilimi da cigaban jami'ar ta hanyar daukar nauyin gina gine-gine da kuma tallafin karatu ga daliban mazabarsa na tsawon shekaru biyar.
Farfesa Bichi ya bayyana cewa, "Muna matukar godiya ga dukkan mahalarta taron kuma muna fatan za su kasance tare da mu har zuwa kammala shirin."
Dangane da batun tsaro a jami’ar, Farfesa Bichi ya tabbatar da cewa an dauki matakan tsaro da suka hada da gina rumfunan tsaro a yankuna daban-daban na jami'ar tare da hadin gwiwar jami’an tsaro daga gwamnatin jiha da kuma Ofishin Mai Ba da Shawara kan Tsaro na Kasa (NSA). Bayan bikin yaye daliban, jami’ar za ta koma babban harabarta na dindindin saboda kyautatuwar yanayin tsaro a yankin.
A kan batun daukar aiki kai tsaye ga dalibai bayan sun kammala karatu, Mataimakin Shugaban Jami'ar ya bayyana cewa jami'ar na daukar ma'aikata ne bisa ga bukatun kowanne sashe. Ya ce, "Sashe ne ke bukatar daukar daliban da suka dace don ci gaba da horar da su yadda ya kamata don taimakawa sashe."