NNPC Ta Kaddamar Da Shirin Gwajin Cutar Daji Kyauta Ga 'Yan Najeriya 3,000
- Katsina City News
- 29 Oct, 2024
- 160
Katsina Times
Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC Ltd) tare da hadin gwiwar Gidauniyar NNPC ya kaddamar da shirin gwajin cutar daji kyauta ga 'yan Najeriya masu karamin karfi domin yaki da yawan mace-macen daji a kasar.
An shirya wannan gangamin mai suna "Sanin Cutar Daji da Gwajin ZSX" tare da hadin gwiwar jami’an lafiya na yankuna daban-daban domin wayar da kan mutane kan cutar daji da tabbatar da ganowa tun farko. Za a gudanar da gwaje-gwajen ne a jihohin Kaduna, Rivers, Ondo, Benue, Imo da Gombe domin tallafawa mutane 3,000 daga yankunan siyasa guda shida na kasar.
Shugabar Gidauniyar NNPC, Mrs. Emmanuella Arukwe, ta bayyana cewa burin wannan gangami shi ne ceto rayuka da kuma kara wayar da kai a fannin kiwon lafiya. Tace yawan mutane na mutuwa daga cutar daji a Najeriya saboda rashin samun gwaji tun da wuri, sannan wannan shirin zai taimaka wajen rage wannan matsala.
A cewar WHO, Najeriya na fuskantar yawan mace-mace sakamakon cutar daji, inda nau'ikan da suka fi yaduwa sune cutar daji ta mama da mahaifa ga mata, da kuma na prostate ga maza.
Gidauniyar NNPC na da burin samar da daidaito a fannin kiwon lafiya domin inganta rayuwar 'yan Najeriya.