ACF Ta Bukaci Dokar Ta-Baci Kan Matsalar Rashin Wutar Lantarki a Arewa

top-news

A cikin makon da ya gabata, mafi yawan jihohin arewacin Najeriya na fama da matsananciyar matsalar rashin wutar lantarki, lamarin da ya janyo tsayawar harkokin tattalin arziki da na zamantakewa. Kungiyar Arewacin Najeriya "Arewa Consultative Forum" (ACF) ta bayyana cewa rashin wutar lantarki a yankin ya kai matsayin barazana ga tsaron kasa, tare da nuna damuwa kan rashin adalci a rarraba wutar.

A cewar ACF, duk da cewa yankin Arewa na samar da kaso mai yawa na wutar lantarki, yana karɓar kaso mafi ƙanƙanta na rarrabawa, inda jihohi da dama ke da babban karancin tashoshin rarraba wuta idan aka kwatanta da Legas, wacce ke da tashoshi guda takwas. Kungiyar ta yi kira ga gwamnati da ta gaggauta daukar matakin gaggawa kan wannan batu domin kare zaman lafiya da tabbatar da adalci a kasar.

Haka kuma, ACF ta bukaci gwamnoni da 'yan majalisar dokoki na yankin Arewa su zage dantse wajen fitowa su nemi daukar mataki kan wannan matsala.