SATIN FARA JARABAWA TA ƘASA: Iyaye da Dalibai Sun Nemi Gwamna Raɗɗa Ya Sake Duba Rufe Makarantun Kiwon Lafiya Masu Zaman Kansu a Katsina
- Katsina City News
- 28 Oct, 2024
- 116
Iyaye, dalibai, da masu ruwa da tsaki sun yi kira ga Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa, da ya duba batun rufe makarantun kiwon lafiya masu zaman kansu da aka yi a faɗin jihar, don gujewa asarar da za ta shafi ɗaliban da ke shirin rubuta jarabawar ƙasa (National Examination).
Kiran ya zo ne a daidai lokacin da wasu ɗaliban ke shirin jarabawar ƙarshe, wanda wata hukuma a matakin ƙasa ke shirya wa, ba jiha ba.
Waɗannan makarantun da aka rufe bisa umarnin Gwamna Dikko, suna jiran kammala aikin tantance su domin fitar da waɗanda ba su cika ƙa’ida ba. Wannan rufewa ya yi wa dalibai ƙalubale, musamman ma ga waɗanda za su rubuta jarabawa a ranar Laraba, 30 ga Oktoba, 2024.
Iyaye sun bayyana cewa ba su ƙalubalanci rufewar makarantun ba; sai dai suna roƙon Gwamna Dikko da ya sassauta umarnin a ba da damar ɗaliban su rubuta jarabawar domin gudun asarar kuɗin da suka kashe da kuma gujewa bata wata shekara guda.
Dalibai sun nuna damuwa kan wannan halin da suke ciki, suna mai cewa idan aka rasa damar rubuta jarabawar yanzu, ba za a iya mayar da lokacin baya ba. Suna fargabar yadda hakan zai shafi karatunsu da rayuwarsu gaba ɗaya.
Masu kira ga gwamnati sun ba da shawarar cewa, idan an kammala jarabawar da za ta ɗauki kwana huɗu kacal, a sake rufe makarantun kafin a ci gaba da tantance su bisa ƙa’ida. Wannan dama, in ji su, za ta karfafa gwiwar dalibai da iyaye wajen cigaba da karatun kiwon lafiya a jihar Katsina.