Rashin Wuta a Arewa Zai Ci Gaba Saboda Matsalar Tsaro – TCN
- Katsina City News
- 25 Oct, 2024
- 210
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya sanar da cewa matsalar rashin wuta da ke addabar yankin Arewa za ta ci gaba saboda kalubalen tsaro da ke hana gyaran wasu muhimman layukan wutar lantarki.
Rashin wutar, wanda ya shafe kwanaki fiye da hudu, ya faro ne bayan wasu ’yan ta'adda sun lalata layin wutar Shiroro-Mando da ke kawo wuta ga jihohin Arewa. Ko da yake TCN ta karkatar da wuta ta layin Ugwuaji-Apir mai ƙarfin 330-kilovolt don rage tasirin matsalar,
wata matsala a wannan layin ya ƙara ta’azzara matsalar.
Injiniya Nafisatu Asabe Ali, Daraktar Gudanar da Tsarin Mulki na TCN, ta bayyana a wani taron sauraron jama’a cewa ko da yake layin na Ugwuaji-Apir na iya ɗaukar megawatt 750, kawai megawatt 350 za a iya isarwa lami lafiya zuwa Kano, Kaduna, da wani yanki na Jamhuriyar Nijar saboda kuntatuwar ƙarfin lantarki.
Duk da cewa TCN na da kayan gyaran da ake buƙata, sun ce ba za su iya ci gaba da gyaran ba har sai an samu sauƙi a lamuran tsaro. A halin yanzu, Majalisar Wakilai ta nemi Ofishin Mai Ba da Shawara kan Tsaro na Ƙasa da ya haɗa kai da hukumomin tsaro don kare muhimman layukan wutar lantarki daga masu lalata su.