Kwamitin Zaɓen Majalisar Dattawa Ya Gudanar Da Taron Shiyyar Arewa Maso Yamma Kan Shigar Matasa da Mata A Harkokin Zabe Da Shugabanci
- Katsina City News
- 24 Oct, 2024
- 223
Auwal Isah (Katsina Times)
Kwamitin Zaɓen Majalisar Dattawa ta Nijeriya ya shirya babban taron kwanaki biyu a shiyyar Arewa maso Yamma da ke mayar da hankali kan doka da yadda matasa maza da mata za su shiga cikin harkokin zaɓe da shugabanci. Taron, wanda ya fara ne a ranar Alhamis, 24 ga Oktoba 2024, ya gudana a jihar Katsina kuma za a kammala shi ranar Juma’a 25 ga Oktoba.
Taron ya samu halartar manyan masu ruwa da tsaki, 'yan siyasa, 'yan fafutuka, da wakilan kungiyoyin fararen hula da suka tattauna kan muhimmancin sauya dokoki da manufofi domin bai wa matasa da mata damar shiga cikakken iko a harkokin zaɓe da shugabanci.
A yayin taron, an gabatar da muhimman lakcoci daga masana daban-daban a fannin siyasa da zamantakewa, inda aka tattauna batutuwan da suka shafi inganta rawar da matasa da mata ke takawa a matsayin jagorori na yanzu da kuma nan gaba. Cikin waɗanda suka gabatar da jawaban akwai Sanata Abdulaziz Musa ‘Yar’adua, Sanata Ireti Kingibe, Sanata Abdul Ningi, Dr. Mukhtar Alkasim, da Dr. Sama’ila Balarabe.
A jawabinsa na bude taron, Gwamnan Jihar Katsina, Dr. Dikko Umar Radda, wanda ya samu wakilcin Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Abdullahi Garba Faskari, ya yi kira ga matasa maza da mata da su shiga cikin harkokin siyasa dumu-dumu domin tabbatar da cewa suna taka rawar gani wajen samar da shugabanci na gari a duk matakan mulki.
"Matasa suna da muhimmiyar rawa a tsarin dimokuradiyya, daga matakin kansila har zuwa na shugabancin kasa. Dole ne a tallafa musu tare da nuna musu hanyar da za su bi don kauce wa fadawa cikin matsalolin da za su iya raunana tasirinsu a siyasance," in ji Faskari.
Sanata Abdulaziz Musa ‘Yar’adua ya jaddada cewa matasa su ne ginshikin samun nasara a duk wani zaɓe, yana mai cewa, "ba za a samu nasarar gudanar da zaɓe ba tare da fitowar matasa ba." Ya kuma kara da cewa, ya kamata matasa su fahimci rawar da suke takawa wajen samar da shugabanci mai inganci domin inganta makomar Nijeriya.
Shi kuwa Sanata Abdul Ningi ya bayyana cewa babu wani shugaba da zai iya cin zaɓe ba tare da goyon bayan matasa ba, inda ya bukace su da su rika shiga harkokin zaɓe cikin tsanaki da kwazo domin kar su bari a mayar da su saniyar ware a tsarin siyasa.
Taron ya kuma samu halartar wakilan kungiyoyin fararen hula daga jihohin Kano, Jigawa, Kaduna, Sakkwato, Zamfara, Kebbi da Katsina. Daga cikin kungiyoyin da suka halarta akwai Kungiyar Masu Sikila Ta Jihar Katsina, Kungiyar Matasan Kiristoci Ta Kasa (CAN) reshen jihar Katsina, Kebbi State Youth Connect Initiative, Ikra Foundation daga Zamfara, da Kungiyar "We-girls."
An yi wa taron kallon wata babbar dama ta dandalin tattaunawa tsakanin ‘yan majalisa da al’umma domin samar da sabbin dokokin da za su bai wa matasa da mata damar taka rawar gani a cikin harkokin shugabanci. Taron ya samu kyakkyawan fata daga mahalarta, wadanda suka nuna gamsuwarsu da yadda ake kara bai wa kowane sashi na al’umma damar shiga harkokin mulki.
An kammala taron ne da cimma wasu muhimman shawarwari da za a yi amfani da su wajen gyara dokokin zabe a nan gaba, tare da tabbatar da cewa matasa da mata sun samu cikakkiyar damar shiga siyasar ƙasa.