Rage Radadi: Mun Karya Farashin Kifin Mu Ne Don Saukakawa Masu Karamin Karfi, -Alhaji Babangida Wayya Sauki Fish
- Sulaiman Umar
- 18 Aug, 2023
- 1347
Shugaban rukunin Sauki Fish, Alhaji Babangida Wayya Shinkafi, ya bayyana dalilinsa na karya farashin kifinsa yayin da ya karyata rade-radin da ke yawo a gari na cewa karya farashin kifin na da nasaba ne da rufe hanyar boda da akayi tsakanin jihar Katsina da Nijar.
Dan kasuwar ya bayyana cewa babu abin da ya shafi sana’ar kifinshi da kasar Nijar kamar yadda ake rade-radi a gari, ya kuma kara da cewa shi sam baya da wajen saida kifi ma a Kasar ta Nijar, ya kuma yi kira ga jama’ar gari da su yi fatali da rade-radin da ke yawo inda ya bayyana hakan a matsayin labarin kanzon kurege.
Tun a kwanakin nan ne dai gidan kifin ya karya farashin kifin nashi yayin da ya zaftare kaso mai tsoka kan farashin kifin nasa, wanda hakan ya sanya mabukata da dama tun daga masu saye da sayarwa da masu amfanin gida cuncurundo a harabar gidan kifin nasa domin mallakar wannan garabasa.
Alhaji Babangida ya ayyana dalilin nashi na yin wannan garabasa yayin da ya bayyana cewa yayi amfani ne da salon kasuwanci inda mutum zai sayi kaya tun yana da sauki sannan ya saida wa al’umma a musamman irin wannan lokacin da suke bukatan taimako. Yin hakan kamar wata dama ce ga masu karamin karfi da basa iya saya da su saya yanzu. Bugu da kari kuma hakan ya samo asali ne tun daga bude kamfanin kifin da akai mashi lakabi da “Sauki Fish”.
“Kowa ya sani cewa yanzu lokaci ne da muke fama da matsalar tattalin arziki, amma maganar ace wai Nijar an rufe boda ba gaskiya bane domin ni babu abin da ya hada sana’a ta da Nijar” inji shi.
A karshe kuma dan kusawan ya yabawa kwastomominshi dake fadin jihar Katsina don irin gagarumar gudummuwar da suke bashi bangaren duk wani kasuwancinshi tun daga na kifi, kaji da dai sauransu.