NOA Ta Kaddamar Da Fara Ayyukan Bunkasa Akidojin Kasa A Katsina.
- Katsina City News
- 18 Oct, 2024
- 340
Daga Auwal Isah, Muhammad Aliy Hafiziy (Katsina Times)
Hukumar nan ta gyaran akida da wayar da kan 'yan Kasa, NOA, ta gudanar da taron kaddamar da fara muhimman ayyukan kimanta Akidojin kasa da sabon taken kasa a matakin jiha da kasa baki daya a jihar Katsina.
NOA ta gudanar da taron kaddamarwar ne a ranar Alhamis din nan a dakin taro na Multipurpose Women Centre da ke Filin Samji, taron da ya samu halartar masu ruwa da tsaki, hukumomi, kungiyoyi da shugabannin al'umma.
Tun farko da yake jawabin manufar taron, shugaban hukumar NOA na kasa, Malam Lanre Issa-onilu wanda ya samu wakilcin shugaban hukumar na Jiha, Alhaji Muntari Lawal Tsagem, ya bayyana taron a matsayi na muhimmancin farfado da Akidojin kasa da kimar kasa ta hanyar sabunta shigar da alamomin kasa a cikin zukatan 'yan kasa don dawo da kishin kasa ga 'yan kasar.
Alhaji Tsagem, ya bayyana sabon aikin da Majalissar kasa ta yarje masu su yi ga 'yan kasa ( na riko da Akidojin kasa) a matsayin wanda zai kai kasar ga kololuwar ci gaba kamar kamar ko ma fiye da sauran takwarorinta.
Zaunawar akidar kasa a zukatan 'yan kasa, da suka hada da kimanta Alamomin Kasa; Tutar Kasa, Taken Kasa, Tambarin Kasa da sauransu, su ne muhimman ayyukan da hukumar ta dukufa yi a yanzu, kamar yadda shugaban hukumar ya bayyana a jawabin nasa.
Da yake nasa jawabi a matsayinsa na babban bako a taron, mataimakin gwamnan jihar Katsina, Honorabul Faruk Lawal Jo6e, ya koka matuka kan yadda kishin kasa ya karanta sosai ga al'ummar kasar.
Bugu da kari, mataimakin na gwamna ya kuma bayyana takaicinsa na yin watsi da tarihinmu da muka yi, inda ya bayyana watsar da kishin kasarmu da tarihinmu a matsayin abin da ya kai mu ga kara tsanantar halin da muke ciki na kuncin rayuwa duk da cewar muna arzikin kasa da yawan al'umma wanda ita kanta al'ummar arziki ce.
Sauran wadanda suka yi Lakca a taron sun hada da Malam Mubarak Adamu daga tsangayar Mulkin jama'a ta Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Hassan Usman Katsina, da kwamishinan 'Yansan jihar, Kwamishinar Mata da sauran shuganannin al'umma.
Taron na NOA har wayau, ya samu halartar hukumomin tsaron 'Yansanda, Jami'an tsaron farin kaya, Jami'an sasantawa da hana laifuka, Jami'an hukumar shige da fice, jami'an hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, jami'an hukumar kiyaye hadurra da sauran hukumomin tsaro.
Sauran Mahalartan sun hada da Wakilan Masarautun Katsina da Daura, Jami'ar hulda da jama'a ta hukumar NOA ta kasa, Hajiya Rabi Muhammad, Wakiliyar Kwamishinar Jin dadin mata, Hajiya Hajara, Kwamishinar Ma'aikatar Ilimin Firamare da Sakandare ta Jiha, Hajiya Zainab Musa Musawa, Mai ba gwamna shawara kan wayar da kan jama'a, Alhaji Sabo Musa da sauransu kungiyoyin al'umma.