Hukumar Gyaran Akida Ta Kira Taron Manema Labarai Kan Inganta Kimar Kasa
- Katsina City News
- 10 Oct, 2024
- 271
Auwal Isah, Zaharaddeen Ishaq Abubakar (Katsina Times)
Muntari Lawal Tsagem state Director NOA Katsina
Hukumar Gyaran Akida ta Kasa, reshen jihar Katsina, wadda ake kira da "National Orientation Agency (NOA)" a turance, ta gudanar da wani taron manema labarai na musamman, domin tattaunawa kan wasu muhimman batutuwa da suka shafi ci gaban kasa da bunkasa kimar al’adun kasa. Taron ya gudana ne a ranar Alhamis, karkashin jagorancin Daraktan Hukumar a jihar, Alhaji Muntari Lawal Tsagem.
A jawabin da ya gabatar, Alhaji Muntari Tsagem ya bayyana cewa, Hukumar ta samu amincewa daga Majalisar Zartaswar Kasa kan wasu muhimman kudurori da za su taimaka wajen dawo da martaba da kima ga alamomin kasa, ciki har da Tutar Kasa, Taken Kasa, da Tambarin Kasa. Ya ce wannan mataki yana daga cikin shirye-shiryen da hukumar NOA ke dauka domin inganta kimar kasa a idon duniya, tare da jaddada muhimmancin fahimtar al’umma game da darajar wadannan alamomi.
A cikin bayanin sa, Tsagem ya nuna cewa, daga yanzu, baitocin farko na taken kasa ne kawai za a rika rerawa a tarukan yau da kullum na hukumomi da kungiyoyi. Haka kuma, rukunin baitocin karshe na taken za a yi amfani da su ne a matsayin addu’o’in bude taruka a hukumance, inda ake ganin hakan zai kara fadakar da jama’a game da muhimmancin hadin kai da fahimtar juna a tsakanin addinai daban-daban a kasar.
Tsagem ya kara da cewa, a manyan taruka na musamman irin su bikin tunawa da ranar samun 'yancin kai, ranar dimokuradiyya, da sauran muhimman bukukuwa na kasa, kacokam din rukunin baitocin uku na taken kasa za su kasance wani bangare na bukukuwan, domin kara nunawa duniya irin kishin da 'yan kasa ke da shi ga kasar su.
Daga karshe, Alhaji Muntari Lawal Tsagem ya jaddada cewa, Hukumar NOA za ta ci gaba da yin aiki tukuru wajen fadakar da al'umma a fadin jihar Katsina da ma kasa baki daya, don tabbatar da cewa an aiwatar da wadannan sabbin tsare-tsare cikin nasara. Hakan, in ji shi, zai taimaka wajen gina kasa mai cike da alfahari da alamominta da kuma tunanin cigaba ga al’umma.