Hakikanin rawar da Katsina ta taka a jarrabawar NECO ta 2024

top-news

Saita bayanai daidai wa daida

Wallafe-wallafe a kafafen sadarwa na baya-bayan nan ga jama’a kan yadda dalibai ‘yan Jahar Katsina suka ci jarabawar Hukumar Jarrabawa ta kasa (NECO), ya sanya ya zama wajibi Gwamnatin Jihar ta mayar da martani ga munanan zarge-zargen da ke nuna darajar ilimin Jihar a cikin mummunan yanayi. Don haka gwamnatin jihar Katsina ta ga ya dace ta warware wadannan kura-kurai don gabatar da hakikanin yadda dalibanmu suka samu abin a yaba musu.

Tun tuni jihar Katsina ta samu rahoton kwazon dalibanta a jarabawar NECO da aka kammala. Rahoton ya nuna ba kawai matsayin daliban a kan wasu fitattun sigogi ba, har ma da bayanai dalla-dalla, wanda ke sauƙaƙa fahimtar masu karatu da masu kallo.  Sabanin rahotannin da wasu kafafen yada labarai ke yadawa na kuskure, jihar mu ta yi nesa da kasancewa a kasa a jerin jadawalin NECO.  A gaskiya muna farin cikin sanar da duniya cewa dalibanmu sun taka rawar gani sosai, wanda hakan ya sanya Katsina a cikin jahohin da suka fi cin jarabawar a Najeriya. 

A mataki na kasa, jihar Katsina ce ta zo ta hudu a jerin sunayen ɗaliban da za su fafata a jarabawar NECO, inda ta samu yawan dalibai 70,842. Tana bayan Kano (147,264), Legas (89,387), da Oyo (80,752). Wannan ya nuna cewa Katsina na da yawan masu shiga jarabawar NECO. Irin wannan yawan shiga ya nuna a fili irin jajircewar jiharmu ta fuskar ilimi da kuma amannar da al’ummarmu suke da ita da tsarin jarabawar NECO.

Abu mafi mahimmanci, ta fuskar cin jarabawar, jihar Katsina tana alfahari da samun matsayi na 6 a duk fadin kasa. Muna da dalibai 29,633 da suka sami cin darussa 5 da sama da haka, ciki har da Lissafi da Ingilishi.  Wannan kyakkyawan sakamako ya sanya mu a gaban jihohi da dama, ciki har da wasu da ke da kwarjini na ilimi a al'adance.  Ya kamata a lura da cewa Legas (65,296), Kano (65,264), Oyo (47,973) Benue (40,379) da Ogun (34,805) ne kadai suka fi Katsina a wannan fannin.

Rawar da muka taka na cin jarabawar na da kyau, musamman idan aka kwatanta da sauran jihohin Arewa. Katsina ta zarce da yawa daga cikin makwabtanta na Arewa, inda ta kafa kanta a matsayin jagaba a fannin ilimi a arewacin Najeriya. Wannan nasarar ba bisa hadari ba ce, sai dai sakamakon saka hannun jari da tsare-tsare a fannin iliminmu da gwamnatin jihar mu ta yi.

In ana magana game da saka hannun jari, Gwamna Dikko Umaru Radda PhD CON ya bayyanar da himmarsa ta fuskar ilimi ba tare da gajiyawa ba. Tun hawansa mulki, Gwamna Radda yana kallon ilimi a matsayin ginshikin gwamnatinsa.  Gwamnatinsa ta aiwatar da wasu tsare-tsare da nufin inganta harkar ilimi a jihar Katsina.  Wadannan sun hada da zuba jari mai yawa wajen horar da malamai da jin dadin su, da inganta ayyukan makarantu a fadin jihar, da aiwatar da sabbin tsare-tsare na koyo don daukar nauyin wasu ’yan asalin jihar Katsina don yin karatu a kasashen waje. 

Sakamakon da muke gani a yau shaida ce ga waɗannan ƙoƙarce-ƙoƙarcen. Tsallen da muka yi zuwa matsayi na 6 a duk fadin kasar, wata shaida ce karara cewa manufofin ilimi na Gwamna Radda ba alƙawura ba ne kawai, amma suna ba da sakamako na gaske, kuma a cikin shekaru masu zuwa ya kamata mu sa ran ganin gagarumin sauyi mai ban sha'awa. 

Yayin da muke mutunta manema labarai da muhimmiyar rawar da suke takawa a dimokuradiyyarmu da hada kan  jama'a, dole ne mu nuna rashin jin dadinmu game da labaran da ke fitowa daga wasu kafafen yada labarai.  Rahoton nasu ba daidai ba ne kawai;  yana iya yin illa ga damarar ɗalibanmu masu himma da kwazo da malamai. Muna kira ga gidajen yada labarai da su tabbatar da gaskiyar labarinsu kafin a buga su. Kamar yadda aka saba, kofofin hukumar yada labarai na gwamnatin jihar Katsina a bude suke ga masu neman sahihan bayanai game da shirye-shiryenmu na ilimi da nasarorin da jihar ta samu.

A yayin da muke murnar nasarar da muka samu a halin yanzu, muna so mu tabbatar wa al’ummar Katsina cewa Gwamna Radda da yake jagorantari gwamnatin ba za ta huta kan lambobin yabon ta ba. Gwamnati dai za ta jajirce wajen ganin ta ingiza Katsina zuwa matsayi na gaba. Mun sa ido a kan shekarun  gaba, kuma tare da ci gaba da sadaukarwar dalibanmu, malamanmu, da iyayenmu, tare da tallafin gwamnati, mun yi imanin cewa wannan burin yana kusa da a cim masa.

Mu ci gaba da wannan tafiya tare, muna murnar nasarorin da muka samu na gaskiya, tare da yunƙurin neman ƙarin nasarorin.  Katsina tana gina gaba ne, kuma al’umma kasa tana lura da hakan!

Ibrahim Kaula Mohammed shine babban sakataren yada labarai na gwamnan jihar Katsina

 5 Oktoba, 2024