Gwamnatin Katsina Ta Kayyade Lita 50 Ga Kowane Mai Mota Da Zai Sha Man Fetur A Faɗin Jihar
- Katsina City News
- 30 Sep, 2024
- 202
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Kwamitin da Gwamnatin jihar Katsina ta Kafa don Kula da Shigowa da rarraba Manfetur a fadin jihar Katsina ya kayyade Lita hamsin ga Masu Motocin hawa na gida da na 'yan kasuwa, a matsayin iya wanda zasu iya saye saboda rage cinkoso a gidajen man.
Kwamitin ya dauki matakin ne don magance koke-koke da suka karu game da yadda ake rarraba man fetur a tashoshin NNPC, Jihar Katsina ta bullo da sabbin tsare-tsare don inganta damar samun mai a tashoshin. Wannan sanarwar ta fito ne bayan tattaunawa tsakanin Shugaban Kwamitin Samar da Man Fetur da Rarraba Shi, Muhammad Lawal Aliyu Daura, da manajojin tashoshin NNPC a ranar Litinin a ofishin sakataren gwamnatin jihar.
Taron, wanda aka shirya bayan korafe-korafe da dama daga jama’a, musamman kan dogayen layuka da karancin mai, ya yi nazari kan matsalolin da aka fuskanta a tashoshin bayan karin farashin man fetur. Babban matakin da aka dauka shi ne shata iyakar sayen man fetur zuwa lita 50 a kowacce mota a tashoshin NNPC. Wannan matakin yana da nufin rage cunkoso a tashoshin da kuma bai wa mutane damar samun man fetur cikin sauki ba tare da bata lokaci ba.
"Kwamitinmu ya yanke shawarar cewa ba wata mota mai zaman kanta ko motar 'yan kasuwa da za ta iya sayen fiye da lita 50 na man fetur a kowanne zango, don tabbatar da saurin hidima da rage cunkoson ababen hawa," inji Daura. Wannan matakin na nufin magance matsalar motocin da suke da tankunan man da ke daukar lita masu yawa, wanda hakan ke jawo jinkiri ga sauran masu sayen man.
Kwamitin, wanda ya kunshi wakilan hukumomin tsaro, ya jaddada cewa za a tura jami’an tsaro domin lura da saukar mai da yadda ake rarraba shi a tashoshin, don tabbatar da gaskiya da adalci a cikin tsarin. Wadannan matakan sun takaita ga gidajen man NNPCL kadai banda na 'yan kasuwa don dawo da oda a tashoshin NNPC da kuma inganta yadda ake rarraba man fetur a cikin Jihar Katsina.