BINCIKEN MUSAMMAN: MALAM DIKKO RADDA ZAI CETO DAKIN KARATU NA JAHAR KATSINA
- Katsina City News
- 25 Sep, 2024
- 199
Muazu Hassan @Katsina Times
Binciken da jaridar Katsina Times ta gudanar ya gano wani yunƙuri da shiri na musamman da Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Radda, yake yi na ceto dakunan karatu na jihar daga faɗawa cikin hali na rashin kulawa, wanda zai kai su ga zama tarkacen tarihi.
Jihar Katsina ita ce cibiyar ilimi, rubutu, fasaha da bincike, kuma ta kasance ginshiƙi na adabi a arewacin Najeriya. Dakunan karatu muhimman wurare ne na bincike, nazari, da adana tarihi, tare da ƙarfafa karatu da ilimi da fasaha.
A lokacin gwamnonin soja ne aka gina dakunan karatu a kananan hukumomi ashirin na jihar, inda aka cike su da littattafai, tare da ɗaukar ma'aikata. Duk da haka, a karkashin gwamnatocin farar hula, ba a ɗauki wani mataki na zamanantarwa da ingantawa ba, wanda ya haifar da koma baya sosai a waɗannan dakunan karatu. Ginin babban dakin karatu na jihar Katsina, wanda aka gina tun lokacin da jihar ke ƙarƙashin Kaduna, shine mafi tsufa da rashin kulawa a faɗin ƙasar nan.
A zamanin gwamnatin da ta gabata, dakin karatun ya fuskanci barazana, har ma an sayar da wani ɓangare daga ciki ga wani ɗan kasuwa, wanda ya gina wani sabon gini a wajen gari. Wannan yunkuri ya kawo cikas ga cigaban dakin karatun.
Da zuwan Malam Dikko Radda, ya soke waccan yarjejeniyar, kuma yanzu ya fito da sabon shiri na inganta da zamanantar da dakin karatu. Wannan aiki zai sa sunan gwamnan cikin tarihin bincike, ilimi, adabi da fasaha.
Dakunan karatu suna tafiya da zamani, kuma bayan adana littattafai, suna kuma kan yanar gizo, suna haɗa kai da sauran dakunan karatu na duniya. Akwai koyarwa, tarurrukan ilimi, da bincike a waɗannan wuraren.
Shekaru fiye da 25 ne aka yi ana watsi da dakunan karatu na jihar Katsina da na kananan hukumomi. Sai dai zuwan Malam Dikko Radda ya kawo mafita. Hatta filin da aka tanada don gina sabuwar cibiyar dakin karatu lokacin gwamnatin PDP an sayar da shi.
Muhimmancin dakunan karatu ya sa har masu kishin ilimi suna gina nasu, misali dakunan karatu na tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo a Otta, da na Janar Ali Gusau a Kaduna, da na Marigayi MD Yusufu a nan Katsina.
A ƙasashen duniya, an zamanantar da dakunan karatu don tafiya da zamani, kamar yadda Dikko Radda yake shirin yi a Katsina. Bugu da ƙari, dakunan karatu suna bayar da horo, gudanar da tarurrukan ilimi, tare da samar da nishadi da shakatawa.
Akwai gidauniyoyi da dama a duniya da suke bayar da tallafi ga dakunan karatu, amma sai sun cika wasu ƙa'idoji. Amma dakunan karatun Katsina sun jima da ficewa daga wannan damar tun shekaru ashirin da suka gabata.
Gyaran dakin karatun zai taimaka wa matasan jihar wajen samun wuraren bincike na gaskiya, ba tare da dogara ga yanar gizo kawai ba.
Wata mata mai muhimmanci a tarihin dakin karatu a Katsina itace Hajiya Hadiza, wacce ta yi aiki a matsayin darakta na dakin karatu. Tana da rawar gani a zamanin gwamnatin soja wajen ƙoƙarin ceto dakunan karatu na jihar.
Tarihi ba zai manta da Alhaji Iro Isansi, tsohon ɗan majalisar wakilai da ya wakilci Katsina, ba. Ya taimaka wajen gina wasu sabbin wuraren ci gaba ga dakunan karatu a lokacin da yake majalisa.
Katsina Times
Www.katsinatimes.com