Tafiyar Matasa Za Ta Zamo Manuniya a Siyasar Najeriya – Hon. Abdulrazaq Dahiru Kaita
- Katsina City News
- 25 Sep, 2024
- 297
A wani taron manema labarai da ƙungiyar Tafiyar Matasa reshen Jihar Katsina ta shirya, shugabanta, Hon. Abdulrazaq Dahiru Kaita, ya bayyana aniyar kungiyar ta fice daga kowace jam'iyya domin tabbatar da nasarar tafiyar matasa a zaben 2027. Wannan taron ya gudana a safiyar Talata, 24 ga watan Satumba, 2024, dakin taro na sakatariyar kungiyar 'Yanjaridu ta Katsina (NUJ)
Hon. Abdulrazaq Dahiru Kaita ya bayyana cewa babban dalilin kafa ƙungiyar Tafiyar Matasa shi ne don tsayawa tsayin daka wajen ganin matasa sun samu cikakken yanci da damar shugabanci, ba tare da an yi amfani da su kawai a matsayin kayan aiki da za a yi watsi da su ba bayan an cimma muradun 'yan siyasa. Ya bayyana cewa matasa sun daɗe suna fuskantar ƙalubale a fagen siyasar Najeriya, inda aka mayar da su kayan amfanin wucin gadi kuma ana watsar dasu bayan amfani.
“Kafa wannan ƙungiyar ya samo asali ne domin mu matasa mu kafa jam'iyyarmu ta siyasa, domin mu tunkari zaben 2027 da karfi, ba tare da dogaro da tsoffin tsarin jam'iyyun da ke wulakanta mu ba," inji Hon. Kaita.
Ya yi karin haske kan yadda ƙungiyar ta ci gaba a Jihar Katsina, inda ya bayyana cewa tafiyar ta riga ta samar da ofisoshi 30 a fadin jihar, wanda 15 daga ciki ke aiki da cikakken karfi. Haka zalika, ƙungiyar tana da shugabannin shiyya guda 20 a kowane yankin sanatan jihar, kuma daga cikinsu 9 sun fara gudanar da ayyukansu na siyasa da tsari.
Hon. Kaita ya bayyana cewa kungiyar ba ta dogara da matasa kaɗai ba, amma ta ƙunshi ƙwararrun 'yan siyasa, mata, da kuma masu bukata ta musamman, wanda hakan ya sa kungiyar ke samun karɓuwa a ko'ina. “Muna kuma nazari da tsara dabarun yadda za mu yi hulɗa da sauran ƙungiyoyin siyasa da ke da manufa irin tamu, a ciki da wajen Jihar Katsina, don ganin mun kawar da irin tsare-tsaren shugabanci da ke tauye damar matasa,” inji shi.
Shugaban ƙungiyar ya yi kira ga matasan Jihar Katsina da su haɗa kai, su cire son zuciya, su jajirce, tare da sanya yakinin cewa nasara tana hannun Allah. Ya ce dole ne matasa su tashi tsaye wajen samun cikakken shugabanci, tare da yin addu'a domin neman nasarar tafiyar.
"Muna rokon matasanmu da su haɗa kai, mu daina rarraba kai, mu tashi tsaye domin tabbatar da samun cikakken shugabanci da zai kawo canji," inji Hon. Kaita.
A karshe, Hon. Kaita ya jawo hankalin manyan 'yan kasuwa, masu ilimi, 'yan siyasa, da duk masu ruwa da tsaki a tafiyar matasa da su tashi tsaye don ganin an cimma burin kafa tafiyar matasan a zaben 2027. Ya kara da cewa lokaci ya yi da matasa za su kafa sabon tarihi a siyasar Najeriya.
“Muna kira ga dukkan al’ummar Jihar Katsina, musamman masu ruwa da tsaki, da su tashi tsaye, domin wannan tafiya ta matasa ta tabbata kuma ta yi nasara,” inji shi.