Farfesa Lugga Ya Yi Kira Ga Gyaran Tsaro Cikin Gaggawa a Taron Cikar Jihar Katsina Shekara 37
- Katsina City News
- 23 Sep, 2024
- 375
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
A lokacin bikin cika shekara 37 da kafuwar Jihar Katsina, da aka gudanar a dakin taro na Katsina Motel, Farfesa Sani Abubakar Lugga, Wazirin Katsina na biyar, ya yi kira akan batun tsaro da mahimmancin gyaran tsarin tsaron a Najeriya. Wannan taron, wanda Kungiyar 'Yan Jarida ta Kasa reshen Jihar Katsina ta shirya, an gudanar da Ƙasidu don tunawa da marigayi Dr. Yusuf Bala Usman.
Farfesa Lugga ya yi tsokaci kan yadda tsaro ya kasance tun zamanin baya a karkashin Daular Musulunci da ta fara daga zamanin Annabi Muhammad (SAW), Daular Usmaniyya, da sauran daulolin Musulunci. Ya nuna cewa shugabanni a tarihi sun kasance suna kula da tsaron jama'a a matsayin wani nauyi na gwamnati. A duk lokacin da aka bar jama’a su kare kansu da kansu, matsalar rashin tsaro za ta karu.
Ya bayyana cewa matsalar tsaro ta zama babbar kalubale ga Najeriya, musamman a Jihar Katsina. Ya ce, "Gwamnatocinmu suna fama da matsalar rashin tsaro a dukkan jihohin Najeriya. Har ta kai wasu gwamnatoci suna kira ga al'umma da su dauki makamai don kare kansu." Ya jaddada cewa a tarihi, daga zamanin Daular Musulunci har zuwa yau, akwai shugabanci da ke kula da tsaro, kuma bai kamata a bar jama'a su kare kansu ba.
Wazirin Katsina ya yi kira ga Mai Girma Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda, da sauran gwamnoni 36 da su yi taro tare da Shugaban Kasa, su sanar da shi cewa daukar nauyin tsaro yana hannunsa a matsayin Babban Kwamandan Rundunonin Tsaro. Ya ce, idan Shugaban Kasa da kwamandojinsa sun kasa magance matsalar tsaro, to ya zama wajibi a gyara kundin tsarin mulki domin bai wa gwamnatocin jihohi damar kafa ‘yan sandansu na jihohi domin kare al'ummarsu.
"Ba za mu iya yarda da cewa jama’a marasa makamai su kare kansu daga wadanda ke dauke da AK-47 ba," Lugga ya gargadi jama’a, yana mai jaddada cewa tsarin tsaro yana hannun gwamnati, ba talakawa ba.
A karshe, ya nuna takaicinsa kan shekaru bakwai da Jihar Katsina ta kwashe tana fama da rashin tsaro, tare da yin kira da a dauki mataki na gaggawa don shawo kan wannan matsala ko kuma a sauya shugabannin da suka gaza wajen tabbatar da tsaro.