Jam’iyyar PDP Ta Rantsar da Sabbin Shugabanninta a Katsina, a Shirye-Shirye na Karɓar Mulki a Zaben 2027
- Katsina City News
- 20 Sep, 2024
- 308
A ranar Alhamis, 19 ga watan Satumba, 2024, jam'iyyar adawa ta PDP a jihar Katsina ta rantsar da sabbin shugabanninta waɗanda aka zaɓa kwanan nan, cikin wani gagarumin taro da ya gudana a ofishin jam’iyyar da ke kan titin Katsina zuwa Kano.
Taron ya samu halartar manyan ‘ya’yan jam’iyyar daga sassa daban-daban na jihar, ciki har da tsohon shugaban riko na jam'iyyar, Alhaji Musa Abdulkarim Makarfi, wanda ya jagoranci rantsar da sabbin shugabannin. A cikin jawabin sa, Makarfi ya jaddada aniyarsa ta kasancewa cikin jam'iyyar duk da ƙalubalen da suka sha fuskanta a baya, yana mai ba da tabbacin cewa za su cigaba da aiki tukuru don ganin jam'iyyar ta samu nasara a gaba.
Ya ƙara yin kira ga sabbin shugabannin da su dage wajen cigaban jam’iyyar, musamman wajen shiri don tunkarar zaɓen 2027, inda ya bayyana cewa wannan zai kasance lokaci mai muhimmanci ga jam'iyyar PDP wajen dawo da mulki a jihar Katsina. Ya ce:
“Yanzu ne lokaci da jam'iyyar PDP ke da bukatar cikakken haɗin kai, domin ba zabe ne kawai muke son lashewa ba, har ma da dawo da martabar jam'iyyar a kowanne mataki na siyasa.”
Barista Ahmad, wanda shi ne ya jagoranci shirin rantsar da shugabannin, ya yiwa sabbin zaɓaɓɓun rantsuwa bisa Dokokin ƙasa da na jam'iyyar don ganin sun cika dukkanin Alkawurran da Tanadin Dokokin ta
A nasa ɓangaren, sabon zaɓaɓɓen shugaban jam’iyyar Hon. Nuruddeen Amadi Kurfi, ya yi jawabi mai ratsa zuciya ga mahalarta taron. Ya yi kira ga ‘ya’yan jam’iyyar da su haɗa kai da juna domin cimma burin su na lashe zaɓen 2027. Ya bayyana cewa lokaci ya yi da jam'iyyar PDP za ta dawo da mulkin jihar Katsina, inda ya ce:
"Jam'iyyar APC mai mulki ta gaza wajen cika alkawuranta ga mutanen jihar Katsina. Yanzu lokaci ya yi da za mu ƙwato mulki domin kawo canji na gari da cigaban al’umma. Na yi imanin cewa da haɗin kan kowa da kowa, za mu iya cimma wannan babban burin."
Hon. Amadi Kurfi ya kuma ƙara yin kira ga dukan shugabannin jam'iyyar a matakai daban-daban, da su mayar da hankali wajen tabbatar da cewa jam'iyyar PDP ta tsaya cik a kowanne lungu da saƙo na jihar. Ya jaddada cewa za su ci gaba da ƙoƙarin ganin sun samar da haɗin kai tsakanin dukkan mambobin jam'iyyar, domin wannan ne kawai zai taimaka wajen karɓe nasara a zaɓen 2027.
Sabbin shugabannin sun nuna ƙwarin gwiwa da alƙawarin yin aiki tukuru, suna mai ba da tabbacin cewa za su gudanar da duk ayyukan su tare da adalci, sadaukarwa da kuma jajircewa wajen cigaban jam'iyyar a jihar Katsina da ƙasa baki ɗaya.
Taron ya ƙare ne da addu’o’i da fatan alheri ga jam’iyyar da kuma cigaban jihar Katsina baki ɗaya.