Gidauniyar Lamido Ta Raba Kayan Makarantar Firamare da Gudanar da Taimakon Lafiya a Tsauri
- Katsina City News
- 20 Sep, 2024
- 469
Gidauniyar Lamido ta raba kayan makaranta kyauta ga yara 1,500 ga makarantu na firamare a garin Tsauri, karamar hukumar Kurfi a jihar Katsina.
Bugu da ƙari, gidauniyar ta gudanar da aikin taimakon lafiya inda aka bai wa mutane 450 masu fama da cututtuka daban-daban kulawa kyauta.
A lokacin bikin raba kayan makaranta da gudanar da aikin lafiya, shugaban gidauniyar Lamido, Alhaji Jabiru Tsauri, ya bayyana cewa aikin taimakon lafiyar ya haɗa da gwaje-gwaje da kuma rabon magunguna kyauta.
Ya bayyana cewa tun bayan kafuwar gidauniyar, ta gudanar da irin waɗannan ayyukan a cikin yankuna da dama a cikin ƙananan hukumomi goma sha ɗaya na yankin Katsina ta Tsakiya.
Alhaji Jabiru Tsauri, wanda shi ne Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Katsina, ya ce aikin taimakon lafiya da raba kayan makaranta wani ɓangare ne na tallafin gidauniyar a bangaren ilimi da kiwon lafiya.
"Ɗaya daga cikin muhimman manufofinmu a Gidauniyar Lamido shi ne ilimi, wanda ya sa muka dukufa wajen tallafa wa ilimi a matakai daban-daban a jihar Katsina.
"Baya ga raba kayan makaranta, littattafai da sauran kayan koyarwa da koyo a makarantu, muna kuma bai wa ɗalibai tallafin karatu.
"Muna ba da nau'i biyu na tallafin karatu ga ɗalibai, bisa ga ƙarfin aljihun iyayensu.
"Muna bai wa wasu ɗalibai tallafin karatu na cikakken tsari, yayin da muke tallafa wa wasu da ragin kuɗi, domin taimakon iyayen da ba su da damar ɗaukar nauyin karatun ‘ya’yansu.
"Manufarmu ita ce tallafa wa waɗannan ɗalibai su yi nasara a karatunsu domin su zama masu amfani ga kansu, iyalansu da al'ummominsu," in ji Tsauri.
Ya ƙara da cewa wannan tallafi yana cikin jerin abubuwan da aka shirya domin bikin nadin sarautarsa ta ‘Lamidon Katsina’ da za a yi masa a ranar Asabar a fadar Sarkin Katsina.
Sauran abubuwan sun haɗa da gasar karatun Al-Qur'ani mai tsarki da aka gudanar a gidan na Lamidon Katsina dake Goruba road cikin birnin Katsina, da kuma addu’o’in musamman domin samun zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa a jihar Katsina, wanda aka gudanar a Masallacin Juma’a na Banu Coomassie.