Gwamnan Katsina Ya Ba Da Tallafin ₦100M Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Jihar Borno
- Katsina City News
- 18 Sep, 2024
- 252
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya ba da gudunmuwar ₦100 miliyan domin tallafa wa wadanda ambaliyar ruwa ta yi wa mummunar barna a Jihar Borno.
Gwamna Radda ya gabatar da takardar ceke din ga Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, yayin wata ziyarar juyayi da ya kai Maiduguri, babban birnin jihar.
“Munzo nan domin mu yi juyayi tare da ku da al’ummar Jihar Borno kan wannan mummunan al’amari na ambaliyar ruwa,” in ji Gwamna Radda, yana mai jaddada tsananin lamarin.
Gwamna Zulum ya nuna godiya sosai ga Gwamna Radda da al’ummar Jihar Katsina kan wannan karamci, inda ya ce gudunmuwar za ta taka muhimmiyar rawa wajen farfado da rayuwar jama’a.
Tawagar Jihar Katsina ta kunshi manyan mutane kamar Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruq Umar; Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Katsina, Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura; da Shugaban Ma’aikatan Gwamnan, Alhaji Abdullahi Jabiru Tsauri.
Wannan taimako ya nuna alamar zumunci da hadin kai tsakanin jihohin Najeriya a lokutan matsaloli.