Matasa Sun Kona Gawarwakin ‘Yan Bindiga Biyu a Kaduna
- Katsina City News
- 17 Sep, 2024
- 326
Wasu matasa sun banka wuta ga gawarwakin wasu mutane biyu da ake zargin ‘yan bindiga ne a Nasarawa-Azzara, yankin karamar hukumar Kachia a Jihar Kaduna.
Rahotanni daga City & Crime sun bayyana cewa sojoji sun kashe wasu ‘yan bindiga uku a maboyarsu da ke kusa da kauyen Azzara a ranar Larabar da ta gabata.
Wani shugaba a yankin, wanda ya bayyana lamarin ga wakilinmu a ranar Lahadi, ya ce gawarwakin biyun an same su a cikin daji da ke kusa da yankin Hayin-Dam.
Wani bijilante mai suna Hassan ya bayyana cewa kafin su isa wajen bayan gano gawarwakin, matasa sun riga sun banka musu wuta.
Kakakin rundunar ‘yan sanda ta Jihar Kaduna, ASP Hassan Mansur, ba mu iya samun sa ta waya ba domin jin ta bakinsa game da lamarin.