Gwamna Dauda Lawal Ya Jaddada Goyon Bayan Gwamnati Ga Sojoji a Zamfara

top-news

Gwamna Dauda Lawal ya tabbatar da jajircewar gwamnatinsa wajen bai wa jami'an soji cikakken goyon baya domin tabbatar da tsaro a jihar Zamfara. 

A ranar Juma'ar da ta gabata, Gwamna Lawal ya karɓi Babban Hafsan Tsaron ƙasa (CDS), Janar Christopher Gwabin Musa, a tsohon ɗakin taron gidan gwamnati da ke Gusau. 

Wani bayani daga mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana cewa Babban Hafsan ya bayyana sunan sabon rundunar haɗin gwiwa ta yaƙi da ta'addanci a yankin Arewa maso Yamma, wacce za a rinƙa kiran ta da "Rundunar Samamen Fansan Yamma." Rundunar na da nufin murƙushe 'yan bindiga a yankin.

Gwamna Dauda ya yaba da ƙoƙarin Janar Musa wajen magance matsalolin tsaro a ƙasar nan, tare da bayyana cewa gwamnatinsa za ta haɗa kai da hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a Zamfara. 

A nasa jawabin, Janar Musa ya gode wa Gwamna Lawal bisa goyon bayan da yake bai wa jami'an tsaro, tare da yabawa da ci gaban da aka samu a jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Gwamnan.