Gwamnan Zamfara Ya Kaddamar da Rabon Magunguna daKayan Kariya A Asibitocin jihar
- Katsina City News
- 13 Sep, 2024
- 276
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya ƙaddamar da rabon magunguna masu muhimmanci, kayan kariya ga ma'aikatan lafiya (PPE), da kayan agajin gaggawa ga asibitoci a faɗin jihar.
An gudanar da taron rabon kayayyakin ne a ranar Alhamis a asibitin kula da cututtuka masu yaɗuwa ta (IDH) da ke Damba, babban birnin jihar, Gusau.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya yi ƙarin haske da cewa, rabon kayayyakin na daga cikin ayyukan da gwamnatin jihar ta ɓullo da shi na inganta rayuwar al’umma.
Sanarwar ta ƙara da cewa, an raba muhimman magunguna da kayan aiki na sama da Naira biliyan ɗaya domin cike giɓin da ake samu a fannin kiwon lafiya a jihar.
A yayin da yake gabatar da jawabinsa a taron ƙaddamarwar, Gwamna Lawal ya bayyana cewa shawarar samar da magunguna da kayayyakin agajin gaggawa wani mataki ne na inganta lafiyar marasa lafiya ta hanyar tabbatar da cewa cibiyoyin kiwon lafiya sun wadatu da kayan aiki.
Ya ce, “Wannan rabon magunguna da kayayyaki na sama da Naira biliyan ɗaya, ba wai kawai shiri ba ne, a’a, wata alama ce ta zahiri na jajircewarmu ga dokar ta-ɓaci da muka ayyana a ɓangaren lafiya da kuma ƙudurinmu na tunkarar ƙalubalen kiwon lafiya gaba-da-gaba. Kwanan nan, mun fuskanci batutuwa daban-daban da suka shafi kiwon lafiya, kuma wannan shiri wani muhimmin mataki ne na ƙarfafa tsarin kula da lafiyarmu.
“Kayayyakin da aka raba suna da muhimmanci don inganta ƙarfin mu na magance matsalolin gaggawa na kiwon lafiya, da hana ɓarkewar cututtuka, da kuma ba da kulawa mai inganci ga masu buƙata. Ya kamata a lura da cewa, saboda jajircewar da wannan gwamnati ta yi na ganin ta taka rawar gani a fannin kiwon lafiya, ina alfahari da cewa jihar Zamfara ba a samu ɓullar cutar 'Shan Inna' ba tun watan Satumbar 2023.
“Don haka ina kira ga masu ruwa da tsaki, ciki har da hukumomin gwamnati, masu samar da kiwon lafiya, da shugabannin al’umma, da su haɗa kai don ganin an ci gaba da samun nasara a dukkan ayyukanmu, da kuma tabbatar da cewa an samu nasara cikin gaggawa a dokar ta-ɓaci da muka ayyana a fannin kiwon lafiya. Na yi imani da cewa, za mu iya cimma burinmu a ɓangaren kiwon lafiya yarw da samar da ci gaba mai amfani ne kawai ta hanyar haɗin kai da aiki tare."
“Bugu da ƙari, ina kira ga al'ummar jihar Zamfara da su yi amfani da albarkatun da aka samar. Ya kamata mu inganta al'adar sanin muhimmantar da harkar lafiyar jiki da kuma sa ƙaimi ga tsarin kiwon lafiyar mu. Ta yin haka ne za mu iya hana yaɗuwar cututtuka, da rage yawan mace-mace, da inganta rayuwar al’ummarmu gaba ɗaya.”
Gwamnan ya ci gaba da nuna jin daɗinsa ga abokan hulɗar ƙasashen waje, waɗanda goyon bayansu da karamcinsu ya sanya aka cimma wannan gagarumin aiki. “Jajircewarku kan harkar mu ta inganta lafiya da rayuwar al’ummar Jihar Zamfara baki ɗaya, abin a yaba ne” in ji shi.