SHEKARU HUDU NA SHUGABANCIN FARFESA ARMAYA’U HAMISU BICHI A MATSAYIN SHUGABAN JAMI’AR TARAYYA TA DUTSIMMA SAI SAN-BARKA
- Sulaiman Umar
- 13 Sep, 2024
- 177
Daga Muhsin Tasi'u Yau
Farfesa Armaya’u Hamisu Bichi gudummawar da ya bayar a vangaren koyo da koyarwa ba za a iyakance ta ba a qanqanin lokaci duba da tun da ya taso gaba xayan rayuwarsa tana cikin farfajiyar koyarwa a jami’a ne. Horon da ya samu ne a shekarun baya shi ya janyo wadannan shekaru hudun nasa suka kasance abin alfahari da tinqaho da godiya da sambarka ga duk wanda ya tsinci kansa a karkashin mulkinsa ko a karatu a makarantar ko aiki ko ma zamanka dan Katsina ko mai kishin Katsina da kishin Arewa. Don kuwa duk wanda yake kishin ilimi da cigabansa yasan Farfesa Armaya’u Hamisu Bichi a jami’ar Tarayya da ke Dutsim-ma lallai kwalliya ta biya kudin sabulu abin da ake buqata an samu har da kari a wadannan shekara hudun.
TAQAITACCEN TARIHIN FARFESA ARMAYA’U HAMISU BICHI
An haifi farfesa a garin Bichi Aji a shekara ta 1969 ya yi makarantar firamare a garin Bichi bayan ya gama ya tafi makarantar sakandaren gwamnati a nan garin Bichi a shekarar1980 bayan ya yi shekara biyu a nan sai ya samu damar tafiya makarantar kimiyya ta Dawakin Kudu. Ya zauna a nan har zuwa 1985. Ya samu damar shiga jami’ar Bayero ta Kano inda ya karanta Applied biology . Bayan ya dawo daga bautar kasa sai ya ci gaba da karatunasa a jami’ar Bayero inda ya yi digirina na biyu da na uku. An dauke shi aiki a shekarar 1995 a matsayin assistant lecturer yana nan har Allah ya kai shi ya na zama farfesa a shekarar 2010. A shekara ta 2012 aka kai shi jami’ar tarayya ta Dutsimma domin ya taimaka wurin bude wannan jami’ar. Alhamdulillahi yanzu an yi shekara hudu Farfesa Armaya’u yana rike wannan shawara.
Daga cikin kyawawan halayyar Farsesa a tattaunawa da muka yi da dalibai da malamai na cikar shekararsa hudu a shugabancin wannan jami’a ga abin da suke cewa:
“Hakika samun shugaba mai hakuri da saukin kai irin na VC sai an tona duk abin da za a zo masa da shi na bacin rai da wuya ka gani a idonsa. Mu kananan ma’aikata in yana mu’amala da har mamaki muke yi don za ka rantse da wasu farfesoshi sa’anninsa yake mu’amala ba da leburorin da ke shara da goge-goge ba ne” cewar Muhammadu Rabe. Shi ma Tanimu Lawal wanda xalibi ne a jami’ar ya bayyana cewa” shekararsa uku a makarantar FUDMA amma in yana bayyana halayyar VC ga abokanansa sai su yi ta mamaki yadda dalibi zai iya zuwa gun VC in yana da matsala kuma ya saurare shi a take kuma ya magance masa. Dabi’ar da VC yake nuna musu su dalibai dabi’a ce ta Uba da ‘ya’yansa. Don haka su kansu malaman makarantar suke bin dukkanin ka’idoji na koyo da koyarwa ba sa wasa da hakkokinsu saboda in har VC ya kama an tauye hakkin dalibi to fa anan za a ga fushinsa.”
A bangaren malamai kuwa sun bayar da kyakkyawar sheda ta yadda Farfesa inda suke cewa “yake kula da dukkan hakkokinsu da ya shafi koyo da koyarwa sannan tunda ya zo bai yarda a ci zarafin malami ba, a kullum kuma yakan karfafa musu gwiwa inda yake ba su tallafi kan dukkan abin da suka bukata. Misali karo karatu ko zuwa conference ko seminer bare kuma promotion wanda tunda ya zo a dai wannan jami’ar ba wanda ya taba kuka da an tauye shi. “Tsare-tsaren jami’ar da sauye-sauyen da ya kawo in dai har kana bibiyar jami’oin na duniya ba ma iya na Nijeriya ba za ka ga yana kamanta standard dinsu. Wannan tsari da ya kawo ya dace da tsarin ilimi na duniya wanda ga duk malamin da ke koyarwa a jami’ar FUDMA wannan abin alfahari ne a gare mu ba wai shi ba”
SAMAR DA SABABBIN KWASA-KWASAI
Lokacin da farfesa Armaya’u ya karbi jami’ar FUDMA suna da faculty guda uku tare a program ishirin ko ma a cikin ishirin din guda uku ne kawai suke da full accreditation amma a wata shida na farko aka samu full accreditation a wadannan goma sha bakwan. Wannan ya bayar da kwari gwiwar bude sashen karatu na babban digiri. Yanzu haka PG school din suna yin program sama da tamanin. Wato daga babu zuwa tamanin. Wannan babbar nasara ce. Daga faculty uku yanzu suna da sha uku daga programe ishirin yanzu suna da sama da dari. Daga cikin faculty din da babu aka samar da su a lokacinsa akwai faculty of Engineering da Faculty of Health sciences da faculty of law da Arabic da Islamic studies duka an samar da su a lokacinsa. A lokacin da farfesa Armaya’u ya zama VC na FUDMA ya tarar da su suna da centre kwaya daya tal amma a yanzu akwai santoci da directorate sama da ishirin.
KWARO KARATU GA MALAMAI
A lokacin Farfesa Armaya’u malaman makarantar FUDMA sama da mutum dari hudu sun tafi karo karatu tsakanin digiri na biyu zuwa na uku a ciki da wajen Nijeriya.
HAKKIN MA’AIKATA
Ma’aikata da ke jami’ar FUDMA ba sa kuka da take hakkinsu saboda ana kula da su yadda ya kamata dukkan hakkinsu ana bayar da su. Dukkan hakkinsu musamman promotion daga shigarsa ofis zuwa yanzu babu malamin da zai ce bai same shi akan kari ba a taba wuce biyu ga watan oktoba ba a yi promotion ba. Lokacin da VC Armaya’u ya shiga ofis farfesoshi hudu ne kaf jami’ar amma a tsakanin shekara hudu yanzu FUDMA tana da farfesa fin ishirin.
GINE-GINE DA KAYAN MORE RAYUWA
Wannan cigaban a bayyane yake a shekara hudu an kawata jami’ar da gine-ine inda kowannan sashe yake zaman kansa kuma da duk abin da ake bukata na kawata wuri don jin dadin dalibai da malamai. An kawo wadatattun kayan aiki an zuba a wadannan gine-gine. Wanda a bangaren gine-gine jami’ar FUDMA za ta iya gwada kwanji da dukkan jami’oin gwamnatin Tarayya da ke kasar nan. An yi sababbin dakunan kwanan dalibai kuma an inganta shi an zuba komai da ya dace don hana dalibai su takura.
KIMIYYA DA FASAHA
A bangaren kimiyya da fasaha, jami’ar tarayya da ke Dutsima-ma ta zama zakaran gwajin dafi a kasa ma baki daya , yadda ta bi sahun sauran takwarorinta a yau wajen amfani da ICT don tallafawa ilimi a zamanance da kuma kirkira da gwaje-gwaje da fasahar sadarwa don dai tafiya da zamani a wanan karnin na 21, da kuma salon ilimin kimiyya na duniya. Wannan yana cikin kokarin Farfesa Armaya’u inda ya dage ba a iya malamai ba har dalibai sun rungumi wannan tsari na ICT inda komai nasu ya koma digital.
DAUKAR MA’AIKATA
A shekaru hudun Farfesa Armaya’u an dauki ma’aikata da daman gaske wadanda wasu bayan an dauke su aikin an tura su karo karatu saboda neman kwarewa sannan da dama suna cigaba da ayyukansu na koyarwa, wadanda kuma su ba aikin koyarwa za su yi (Non-acadamic) ba sun cigaba da aikinsu yadda ya kamata. Wadatattun ma’aikata da FUDMA take da su ya taimaka kwarai wajen cigaban kowanne bangare a jami’ar don haka ta zama abin kwaikwayo ga sauran jami’oi sa’anninta da ma wadanda suke gaba da ita a samuwa.
HARKOKIN TSARO
Da yardar Allah da kuma qoqari da jajircewar shugaban jami’ar tarayya ta Dutsim-ma tsaro ya samu a jami’ar inda ya samu hadin kan jami’an tsaro da malamai da dalibai inda ya umarci kowanne bangare yake mu’amala da tuntuba ga kowanne bangare tare da bayar da goyon baya yayin da kowanne bangare ya bukaci hakan. Wannan hadin kan da ya samu babban nasara ce musamman a bangaren tsaro.
TABBATAR DA DA’A DA TARBIYYAR DALIBAI
Farfesa Arma’yau na nuna tarbiyya hakkin malamai ce bayan iyaye don haka ya sa ido sosai tare da kafa wasu dokoki a jami’ar wadanda za su taimaka wurin tarbiyya da kare daliban wurin afkawa abubuwa na assha. Ya Tabbatar da kula da irin sutura da dalibai za su saka na mutumci da da hana shan taba da sauran kayan da suke saka maye, jan kunnen yaran kan shiga kungiyoyin asiri da duk wani abu na kaucewa addinai da al’adu. Misali lalata ko karuwanci .
VANGAREN SUFURI
Kafin zuwan farfesa Armaya’u jami’ar Fudma tana fama da matsalolin sufuri inda da malaman da daliban kowa yana dandana kudarsa kan sufuri musamman daga tsohon matsugunnin jami’a zuwa sabon matsugunninta. Zuwan Farfesa Armaya’u ya mayar da wannan matsalar tarihi a tsahon shekara hudu. An samar da motoci bas-bas kuma kowacce an samar mata da tsaro yayin da ake zirga-zirga da dalibai tsakanin ciboyoyin nazari da ke jami’ar a sabon mutsugunni ko a tsohon wuri. (New compus da old compus)
KUNGIYOYIN DA KE JAMI’A DA ZABE NA SHUGABANCI NA DEPARTMENT
Kungiyoyi da yin zabe tsakanin malamai yayin zabar HOD yana da tasiri kwarai wurin cigaban jami’a da dorewar adalci don wannan damar ce me bayar da ‘yancin zabar cancanta. A baya shugaban jami’a ne ke da alhakin zabar da HOD amma zuwan Farfesa Armaya’u ya mayar malamai da ke sashe suke zabar abin da ya dace. A baya Farfesa Armaya’u ya sami Fudma ba ta da qungiya ta ma’aikata amma da ya zo sai ya bayar da damar tare da ba su gudummawa suka buxe qungiyoyinsu.Su malaman jami’a aka buxe ASUU sai manyan ma’aikata na makaranta suka bu]e SANUU sai qanannan ma’aikata suka bude NASUU sai kuma ma’aikata na kimiyya suka bu]e nasu NAKT wannan ya taimaka kowa ya samu bangaren da zai zauna karkashin wata inuwa wato dai majingina.
SAMUN GRAND
Daliban FUDMA saboda dama da suka samu da ingantacciyar koyarwa da samun sararin koya da suka yi cikin nutsuwa sun samu grand da daman gaske daga ciki da wajen kasar nan haka sun samo kyaututtuka daga kasashen waje. Misali yanzu haka akwai dalibin FUDMA da yake kasar Amurka wanda ya ciyo grand da yawa haka sun samu daga south Africa daga da dai gurare da daman gaske.
Don haka shekaru hudun Farfesa Armaya’u Hamisu a matsayin shugaban jami’ar Tarayya ta FUDMA sai san barka.